Ran 15 ga wata, mataimakawa na ministan harkokin waje na kasar Sin Mr. Cui Tiankai da ke ziyarar aiki a kasar Iran ya yi wa kafofin yada labaru bayanin cewa, kasar Sin tana fatan kasar Iran za ta yi amfani da zarafi za ta amsa shirye-shiryen da kasashe 6 suka bayar kan batun nukiliya na kasar Iran.
Mr. Cui ya kara da cewa, har kullun bangaren kasar Sin yana tsayawa tsayin daka kan warware batun nukiliya na kasar Iran cikin lumana ta hanyar yin shawarwarin diplomasiyya. Saboda haka, bangaren kasar Sin yana fatan bangaren kasar Iran zai amsa shirye-shiryen da kasashen 6 suka bayar ta cikakkun hanyoyi, a sa'i daya kuma, yana fatan sauran bangarorin da abin ya shafa za su dauki matakan da suka wajaba wajen samar da sharadi ga mayar da shawarwari.(Tasallah)
|