Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-08 17:03:29    
Dutsen Kunlun

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan dutsen Kunlun, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, mutane sun kara jin dadin ganin sabbin ni'imtattun wuraren Sanxia na kogin Yangtse.

Dutsen Kunlun ya tashi daga tudun Pamier, tsawonsa ya kai kilomita dubu 2 da dari 5, kuma matsakaicin tsayinsa ya kai mita dubu 5 da dari 5 zuwa mita dubu 6 daga ?eburin teku, kolinsa shi ne dutsen Bugedaban, wanda tsayinsa ya kai mita dubu 6 da dari 8 da 60 daga leburin teku. Ruwan tabki yana da tsabta, haka kuma ana iya ganin tsuntsaye da kuma namun daji masu yawa a nan. An yi shekara da shekaru ana yin kankara mai taushi a duwatsun Yuxu da Yuzhu, har ma sai ka ce wadannan duwatsu 2 sun sanya fararen riguna, gajimare da tukukin hazo suna tafiya a tsakanin duwatsun 2. Idon ruwa na Kunlun yana zaune a gabar kogin Kunlun ta arewa, wanda idon ruwa ne mafi girma da ba ya daskarewa har a lokacin dari a cikin dutsen Kunlun, ruwa mai yawa yana fitowa daga wannan idon ruwa lami lafiya, sababo haka, a kan yi kankara mai taushi a watan Yuni a nan. Ruwan da ake samu daga wannan idon ruwa ruwa mai kyau ne kuma na kunshe da abubuwa masu amfani a jiki. A sashen tsakiya na kogin Geermu, wanda ya tashi daga dutsen Kunlun, akwai hayi masu tsayi, mutane suna jin dadin ganin wadannan ni'intattun wurare.

Dutsen Kunlun yana da muhimmanci sosai a cikin tarihin al'adun kabilar kasar Sin, ana kiransa kakan kakamu dukan duwatsu, inda masu bin darikar Kunlun na addinin Taoism na kasar Sin suka kafa babban zaurensu a nan a karshen shekaru 60 na karni na 17 da suka gabata.

Wurin ketare duwatsu na dutsen Kunlun yana kudu maso yammacin lardin Qinghai na kasar Sin, sa'an nan kuma, hanyar dogo da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin ta ratsa yankin tsakiya na dutsen Kunlun, saboda haka, fasinjojin da ke cikin jiragen kasa su kan iya jin dadin ganin kankara mai taushi a watan Yuni. Idan masu yawon shakatawa sun tsaya a wurin ketare duwatsu na dutsen Kunlun suna iya hangen nesa, suna iya ganin cewa, dutsen Kunlun yana da tsawo tun daga gabas zuwa yamma, ana yin kankara mai taushi, sai ka ce wani dragon irin na kasar Sin na farin dutsen lu'ulu'u yana kwance a nan.(Tasallah)