Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-08 15:42:18    
Kasashen Larabawa sun kara daidaituwa, domin magance kalubalen da rikicin da ake yi a tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila ke kawowa

cri
Ran 7 ga wata a birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon, an kiran taron gaggawa na ministocin harkokin waje na kungiyar tarrayar kasashen Larabwa. Domin magance kalubalen da rikicin da ake yi a tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila ke kawowa, kasashe daban daban da ke hallartar taron sun kara daidaituwa, sun nuna matsayinsu na goyon bayan gwamnatin kasar Lebanon, da adawa da harin da kasar Isra'ila ke yi, kuma sun tsaida kudurin da ke da nasaba.

Amur Moussa, babban sakataren kungiyar tarrayar kasashen Larabawa ya shugabancin taron. Fouad Siniora, firayin ministan kasar Lebanon, da ministocin harkokin waje na kasashen Larabawa 17 sun halarcin taron. Gaba daya sun jaddada cewa, suna goyon bayan shiri mai sharuda 7 game da warware rikicin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila da gwamnatin Lebanon ta gabatar, kuma wannan ya zama dinkuwar matsayin da kasashen Larabawa ke tsayawa a kai wajen magance rikicin Lebanon da Isra'ila.

Gwamnatin Lebanon ce ta gabatar da shiri mai sharuda 7 dangane da matsalar kasashen Lebanon da Isra'ila a taron duniya na Rome da aka kira a karshen watan da ya wuce, shirin yana kunshe da abubuwa kamar haka: yin musayar fursunoni tsakaniin bangarorin Lebanon da Isra'ila; sojojin Isra'ila su janye jiki har zuwa gefen Isra'ila na "Layin shudi"; masu gudun hijira su koma gidajensu; a mai da gonar Sabaa da Isra'ila ta mamaye a karkashin shugabancin M.D.D.; sojojin gwamnatin Lebanon su kula da duk kasar; kara sojojin M.D.D. na wucin gadi da ke Lebanon; da kuma M.D.D. ta sa ido kuma ta aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kasashen Lebanon da Isra'ila suka daddale a shekarar 1949.

Bayan haka kuma, taron gaggawa na ministocin harkokin waje na kungiyar tarrayar kasashen Larabawa sun tattauna a kan shirin kuduri dangane da warware rikicin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila da kasashen Amurka da Faransa suka gabatar ga kwamitin sulhu na M.D.D. a cikin 'yan kwanakin da suka wuce. Ko shakka babu, shirin nan yana goyon bayan kasar Isra'ila, sabo da haka, taron ya tsaida kudurin aikawa da wata kungiyar wakilai da nan da nan ta je babbar hedkwatar M.D.D. da ke birnin New York, domin sanar da matsayin da kasashen Larabawa suka dauka, da kuma yin kokari kan gyara shirin kudurin. Bayan haka kuma, Mr. Moussa, babban sakataren kungiyar tarrayar kasashen Larabawa zai shirya kan taron shugabanni na gaggawa game da matsalar Lebanon, da kuma tsara wani hakikanin shirin taro.

Manazarta sun nuna cewa, ko da ya ke wannan taron gaggawa na ministocin harkokin waje na kungiyar tarrayar kasashen Larabawa ya yi kokari sosai, kuma ya samun ra'ayi daya a duk fannoni, amma ba ya da amfani sosai kan warware matsalar rikicin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila. Da farko, kasasshen Amurka da Isra'ila suna da muhimmin amfani kan matsalar rikicin. Tun daga farko, kasar Amurka tana goyon bayan Isra'ila da ta dauki matakin soja. Sabo da haka, zai yi wuya Larabawa su iya shawo kan rikicin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila. Na biyu, ban da kasar Sirya, sauran kasashe ba su iya kawo tasiri sosai ga kungiyar Hezbollah ta Lebanon ba.

Amma, a sa'i daya kuma, manazarta suna ganin cewa, kasashen Larabawa su ma suna da amfani kan matsalar nan. Ran 7 ga wata, Philippe Bouste-Blazy, ministan harkokin waje na kasar Faransa ya ce, kasar Faransa ta riga ta bukaci kasar Amurka da ta jinkirtar da lokacin gabatar da shirin kuduri dangane da warware hargitsin Lebanon ga kwamitin sulhu na M.D.D., domin gyare shi bisa ra'ayin kungiyar tarrayar kasashen Larabawa da gwamnatin Lebanon. Ana sa ido domin ganin kasashen duniya da su iya mayar da martani mai yakini kan kokarin da taron gaggawar ya yi kan warware rikicin da kasashen Lebanon da Isra'ila ke yi. (Bilkisu)