Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-07 21:25:57    
Shirye-shiryen talibijin na digital sun fara shiga zaman rayuwar jama'ar kasar Sin

cri

Yanzu sai mu ci gaba da shirinmu mai farin jini na "Bunkasuwar kasar Sin". Lokacin da ake ambata shirye-shiryen talibijin na digital, a kan dauka cewa su shirye-shirye ne masu saukin ganewa kuma masu dadin kallo. A hakika dai, ba ma kawai akwatunan talibijin na digital suna da irin wannan inganci ba, har ma masu kallon TV za su iya samun labaru iri iri masu yawan gaske da suke bukata kuma suke shafar zaman rayuwar jama'a daga akwatunan talibijin na digital. Yanzu a wasu biranen kasar Sin, ana sayen gidaje da motoci da neman likitoci da sayen kayayyakin masarufi da kuma yin cinikin takardun hannun jari ta shirye-shiryen talibijin na digital. A cikin shirinmu na yau, za mu bayyana muku halin da ake ciki a kasuwannin samar da labaru a akwatunan talibijin na digital a nan kasar Sin.

Tsoho Wang Qingpu wanda yake da shekaru 77 da haihuwa yana da zama a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin. Shi da matarsa su kan kalli TV kowace rana. Yau da shekara 1 da ta gabata, talibijin digital ya fara shiga zaman rayuwarsu. Abun da suka ji murna a kai shi ne, irin wannan talibijin na digital yana samar da labaru game da yadda za a iya samun sabbin litattafan da aka wallafa. Sabo da haka, sun iya sayen litattafan da suke so cikin sauri. "A kan talibijin na digital, ana bayar da jerin litattafan da ake sayar da su cikin sauri. Idan na ga akwai littafin da nake so, sai na je na saya. Wannan abu ne mai sauki kwarai."

Lokacin da talibijin na digital yake samar wa tsofaffi hidimomi iri iri, yana kuma ba da hidimomi iri iri ga wadanda suke da aikin yi. Kamar misali, idan kana son sayen shinkafa, sai ka kunna talibijin na digital. Bisa labarun da aka bayar a tashar talibijin na digital, kana iya zaben wane irin shinkafa da kake son saya da nauyin da kake bukata, sannan kuma ka tabbatar da su. Shi ke nan, bayan kimanin rabin awa daya, za a kai shinkafa da kake so a gidanka.

An bayyana cewa, yanzu a nan kasar Sin ana tsara da watsa da kuma sufurin shirye-shiryen talibiji ta hanyar digital. Amma domin yawancin akwatunan talibijin da ake amfani da su akwatunan talibijin ne irin na tsohon yayi. Sabo da haka, babban aikin sa kaimi wajen karbar shirye-shirye na talibijin na digital shi ne yaya akwatunan talibijin irin na tsohon yayi za su iya karbar irin wadannan shirye-shirye na digital. Hanyar da ake daidaita wannan matsala kuma ake bi ita ce, an sa wani karamin akwatin inji a kan akwatin talibijin irin na tsohon yayi. Sakamakon haka, akwatin talibijin irin na tsohon yayi zai iya kama shirye-shiryen digital, irin wannan akwatin talibijin na tsohon yayi ma ya zama wani akwatin da ke samar da labaru iri iri da suke shafar zaman rayuwar jama'a a fannoni daban-dabam.

Lokacin da yake tabo sharadi mai rinjaye na talibijin na digital, Mr. Zheng Xiaolin, mataimakin babban direktan kamfanin talibijin na digital na birnin Hangzhou ya ce, "Idan an kwatanta irin wannan talibijin na digital da talibijin irin na tsohon salo, hanyar sufurin shirye-shiryen talibijin na digital ta fi fadi. Akwatin talibijin irin na tsohon salo ya iya kama kananan tasoshin talibijin sama da goma, amma akwatin talibijin na digital yana iya kama kananan tasoshin talibijin daruruwa. A sa'i daya kuma, ingancin shirye-shiryen talibijin na digital da aka samu ya fi kyau. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, za a iya kara yawan shirye-shirye ta hanyar sufurin talibijin na digital. A da, an kalli shirye-shiryen da gidan rediyo mai hoto ya watsa kawai, amma, a nan gaba, za a iya zabar shirye-shiryen da ake bukata a kan akwatin talibijin na digital."

Kamar yadda ake yi a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin, ya zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta kebe wurare da birane 50 domin yin gwajin mayar da akwatin talibijin irin na tsohon salo zuwa ga akwatin talibijin irin na digital. A wasu birane an riga an samar da hidimomi iri iri ga jama'a a kan akwatin talibijin na digital. Mr. Zheng Xiaolin yana ganin cewa, akwatin talibijin injin sadarwa ne da jama'ar kasar Sin suka fi yin amfani da shi, aikin sa kaimi wajen yin amfani da akwatin talibijin na digital yana da boyayyen karfi. Mr. Zheng ya ce, "Akwatin talibijin na digital wata kasuwa ce da ke samar da labaru iri iri. Ya kamata mu samar da hidimomi iri iri a kan akwatin digital. Alal misali, muna samar da hidimar yadda za a samu labaru da yin musayar kudade da kuma hidimar yadda za a yi ciniki a kan akwatin talibijin na digital. Jama'a za su samu sauki sosai lokacin da suke yin amfani da akwatin talibijin na digital." (Sanusi Chen)