Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-07 17:48:55    
Kasar Sin ta gyara dokokin shari'a don samun tabbaci ga bunkasa aikin ba da ilmin tilas na kyauta bisa daidaici

cri

Kwanan baya kasar Sin ta gyara "dokar ba da ilmi tilas kuma kyauta". Bayan gyarar da aka yi dokar ta tabbatar da samar da gatanci ga kowa wajen samun ilmi tilas kuma kyauta, da tabbatar da "samun ilmi tilas a kyauta". Sabuwar dokar kuma ta tsai da tsarin samun tabbaci ga kudin da za a ware domin tafiyar da wannan aiki, kuma za a nuna gatanci ga kauyuka wajen samar da albarkatun ba da ilmi. Wannan dokar shari'a za ta samar da gatanci ga 'yan makarantun sakandare da na firamare wadanda yawansu ya kai miliyan 180 da iyalansu na kasar Sin, kuma za su samu tabbataci sosai ga tabbatar da aikin ba da ilmi na farko. To jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayani da wakilinmu ya rauwaito mana dangane da wannan labari.

Kasar Sin tana tafiyar da tsarin ba da ilmin tilas na makarantu masu tsarin karutu na shekaru 9, bisa "dokar ba da ilmin tilas na kyauta" da aka tsayar kafin shekaru 20 da suka wuce, an ce, 'yan makarantun da suka samu irin wannan ilmi ba su biya kudin karatu ba, amma ya kamata su biya kudin zaman yau da kullum. Amma hakikanin halin da ake ciki shi ne, sabo da rashin goyon bayan da sassan ba da ilmi suka samu daga wajen gwamnatin tsakiya wajen kudi, shi ya sa suka mai da aikin kara samun kudin zaman yau da kullam da ya zama muhimmiyar hanyar da suke bi domin samun karuwar tattalin arziki domin tafiyar da harkokin makarantu yadda ya kamata, wannan ya sa yaran wasu iyalai masu talauci musamman ma iyalan kauyawa suka kasa kammala aikin samun ilmin tilas.

"Abu mafi ma'anar tarihi" da aka gyara cikin dokar ba da ilmin tilas na kyauta a wannan gami shi ne, an tsai da cewa kasar Sin "ba za ta karbi kudin karatu da na zaman yau da kullum wajen aikin ba ba ilmin tilas na kyauta ba." Dokar kuma ta tsai da cewa, aikin ba da ilmin tilas na kyauta wani sha'anin jama'a ne wanda dole ne a samu tabbaci ga yin sa. Mr. Zhou Jixian, ministan ba da ilmi na kasar Sin ya bayyana cewa, za a shigar da kudin ba da ilmin tilas na kyauta cikin kasafin kudin da gwamnatin tsakiya da na wurare daban-daban za su dauki nauyin biyan su tare. Ya ce, "Sassan kula da aikin ba da ilmi na gwamnatin gunduma su ne suka tsara kasafin kudinsu, kuma za su nuna gatanci ga makarantun kauyuka da makarantu marasa karfi na birane, majalisar gudanarwa da gwamnatocin wurare daban-daban dake sama da matakin gunduma za su ware kudin musamman domin ba da taimako ga kauyuka da sauran wurare marasa ci gaba wajen tattalin arziki domin tafiyar da aikin ba da ilmin tilas na kyauta. Gwamnatoci na matakai daban-daban kuma za su ba da gudummawa ga 'yan makarantun da suka zo daga iyalai masu talauci ta hanyoyi daban-daban don kada su rasa damar zuwa makaranta sabo da wahalar tattalin arzikin da suke sha."

Madam Chen Xiaoya, mataimakiyar ministan ba da ilmi na kasar Sin ta bayyana cewa, dokar da aka gyara ta tsai da dokokin samun tabbaci ga yaran da suka isa shiga makaranta da su samun ilmin tilas na kyauta bisa daidaici, da samu sauki ga yaran iyalai masu kai da kawowa su shiga makaranta da kara dora nauyin da ke bisa wuyan gwamnatoci. Ta ce, "Dokara da aka yi mata gyara ta yi tsare-tsare sosai ga gabatar da sharudan ba da ilmi bisa daidaici ga 'ya'yan manoma 'yan kodago da na mutanen da suke aikin kogago cikin birane."