Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-06 18:45:24    
Kungiyar gaggauta demokuradiyya ta kasar Sin

cri

Kungiyar gaggauta demokuradiyya ta kasar Sin wata jam'iyyar siyasa ce wadda take hade da masanan ilmi da ke da ikon wakilci wadanda kuma ke dukufa kan ayyukan ba da ilmi da al'adu da dabi da kimiyya da fasaha, wadda kuma take da halin musamman na kawancen siyasa, kuma ta dukufa kan aikin raya zaman gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, ita kuma wata jam'iyya ce da ke shiga cikin harkokin kasa ta hanyar hadin gwiwa a tsakaninta da jam'iyyar da ke rike da mulkin kasa wato J.K.S. kuma wata jam'iyyar demokuradiyya ce da ke cikin dunkulalliyar kungiyar gwagwarmaya ta kishin kasa wadda ke karkashin shugabancin J.K.S.

Muhimman ubannin kafa kungiyar gaggauta demokuradiyya ta kasar Sin su ne Zhou Jianren da Xu Guangping da Lei Jieqiong. A lokacin yakin dagiya kan harin Japan, kungiyar ta hada kanta da 'yan J.K.S. don yin yakin da ceton kasa, bayan samun nasarar yakin kuma ta yi kokarin shiga cikin kamfen din neman samun demokuradiyya. An kafa kungiyar gaggauta demokuradiyya ta kasar Sin da gaske a ran 30 ga watan Disamba na shekarar 1945 a birnin Shanghai.

A watan Satumba na shekarar 1949, wakilan kungiyar gaggauta demokuradiyya ta kasar Sin sun halarci taro na farko na dukkan wakilan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta farko ta jama'ar Sin, kuma sun shiga aikin tsara tsarin ka'idojin tarayya. Cikin "tsarin dokokin kungiyar gaggauta demokuradiyya ta kasar Sin" da aka zartar a gun taron wakilan duk kasa na 6 na kungiyar da aka yi a ran 28 ga watan Nuwamba na shekarar 1988, an tsai da sabbin dokoki kan hali da tsarin ka'idojin siyasa na kungiyar.

Tsarin dokokin ya tanadi cewa, kungiyar gaggauta Demokuradiyya ta kasar Sin wata jam'iyyar siyasa ce wadda ta dukufa kan aikin raya zaman gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, ita kuma wata jam'iyyar demokuradiyya ce wadda take da halin musamman na kawancen siyasa da ke cikin dunkulalliyar kungiyar gwagwarmaya ta kishin kasa wadda ke karkashin shugabancin J.K.S.

Zuwa watan Yuni na shekarar 1997, yawan mambobin kungiyar ya karu har ya kai fiye da mutane dubu 65.

Shugaban kungiyar gaggauta demokuradiyya ta kasar Sin na yanzu shi ne Xu Jialu. (Umaru)