Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-28 09:35:47    
Wassu labaru game da wasanin motsa jiki (22/06-28/06)

cri

Jama'a masu sauraronmu, barkanku da war haka. Yau ma ga shi Allah ya sake hada mu a wannan shiri namu mai ban sha'awa na wasannin motsa jiki, wanda mukan gabatar muku a kowace ranar Laraba bayan labaru. Saboda haka, sai ku karkade kunnuwanku don jin labarun da muke dauke da su tukuna, daga baya akwai wani bayanin musamman.

A kwanakin baya ba da dadewa ba, an kammala budaddiyar gasar wasan kwallon tenis ta Ordina da aka yi a kasar Holland. ' Yan wasa su Zhenjie da Yanzi daga kasar Sin sun samu lambar zinariya a wasan tsakanin mata bibbiyu. Kuma wannan shi ne karo na 4 da suka zo na daya a gun irin wannan wasa bayan budaddun gasanni na Australiya da Jamus da kuma Morocco da aka yi.

Har ila yau ba a tabbatar da cewa ko shahararren dan wasa mai suna Yao Ming zai halarci gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kwando da za a yi a watan Agusta na shekarar da muke ciki ba ko a'a . Shugaban hukumar wasan kwallon kwando ta kasar Sin Mr. Li Yuanwei ya sake nanata ,cewa ko kusa hukumar wasan kwallon kwando ta kasar ba za ta kalubalanci dan wasa mai suna Yao Ming da ya shiga wannan gasa idan bai warke sosai ba. Yanzu, Yao Ming yana kishin halartar wannan gagarumar gasar da za a yi yayin da yake yin horo kamar yadda ya kamata domin neman warkewa tun da wuri.

A ran 22 ga watan Yuni, kwamitin wasannin motsa jiki na kasa da kasa ya shelanta, cewa birnin Salzburg na kasar Austria, da birnin Pyeongchang na kasar Korea ta Kudu da kuma birnin Sochi na kasar Rasha sun samu shiga zabe a zagaye na karshe da ake yi domin neman shirya taron wasannin motsa jiki na Olympic na yanayin sanyi da za a yi a shekarar 2014.

A ran 23 ga watan Yuni, an bude bikin al'adu na 4 na Olympics na " Shekarar 2008 a Beijing" . Nan da wata mai zuwa, za a gudanar da harkoki iri 28 dake bayyana babban taken wasannin Olympics, wadanda kuma suka hada da harkar wasannin al'adu da na motsa jiki na jama'a, da nune-nunen sinema da na T.V, da shirya dandalin tattaunawa, da harkar nuna wasannin fasaha, da shirya gasar kara wa juna sani, da gudanar da wasannin fasaha na nakasassu, da samari matasa da kuma yara manyan gobe.

A kwanakin baya ba da dadewa ba, Cibiyar ba da agaji ta birnin Beijing ta shelanta, cewa za a kafa wata cibiyar ba da jagoranci mai lamba 120 ga aikin jiyya cikin gaggawa a lokacin da ake yin taron wasannin motsa jiki na Olypmpics na Beiijing a shekarar 2008.( Sani Wang )