Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-27 17:17:56    
Ana kokarin kare muhalli wajen shimfida hanyar jirgin kasa ta Qinghai-Tibet ta kasar Sin

cri
Nan gaba kadan ba da dadewa ba, za a fara aiki da duk hanyar jirgin kasa mai tsawon kilomita 1956 da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin. Tun lokacin da aka fara shirin gina wannan hanyar jirgin kasa a kan duwatsu mafi tsayi a duniya, aikin ya jawo hankulan mutane kwarai. Ban da wahalhalu da za a sha wajen yin aikin nan, kuma kalubale mafi tsanani da ake fuskanta shi ne kare muhalli a wurare da za a shimfida wannan hanyar jirgin kasa.

Akwai wani tafki mai fadin muraba'in kilomita 300 wanda ake kira "Cuona" yana da nisan kilomita sama da 400 daga arewacin birnin Lhasa, fadar gwamnatin jihar Tibet ta kasar Sin. A wurin ne ake da tsuntsaye da ake kira "SWAN" da "CRANE" a Turance da barewa irin na Tibet da sauran naman daji masu daraja ke zama.

A lokacin da ake shimfida hanyar jirgin kasa a bakin tafkin nan, an yi kokari sosai wajen kare muhalli. Malam Yan Beizun, wani jami'i mai kula da aikin shimfida hanyar nan ya nuna wata katanga mai tsawon sama da kilomita 20 da aka gina ta da buhunhunan rairayi, ya ce, "matakai da muka dauka wajen hana gurbata ruwan tafkin "Cuona" shi ne gina wata katanga da buhunhunan rairayi don ba da tabbaci ga kare ruwa mai tsabta a cikin tafkin nan"

A wurare da ake shimfida wannan hanyar jirgin kasa, ya kasance da gandayen daji 11. Daga cikinsu, akwai wani gandun daji da ake kira "Kekexili" ya shahara sosai a kasar Sin, inda namun daji kamar bareyi da jakai da shanu irin na Tibet da sauransu su kan yi kai da komawa. Sabo da haka yayin da ake aikin shimfida hanyar jirgin kasa, an kebe hanyoyi sama da 30 musamman domin wadannan namun daji su bi. Malam Cao Yuxin, babban injiniya mai kula da aikin gina sashen hanyar jirgin kasa a gandun daji na "Kekexili" ya bayyana cewa, "a watan Yuni na shekarar 2002, akwai dimbin bareyi irin na Tibet da za su bi ta gandun daji na "Kekexili". Ko da yake wannan lokaci lokaci ne mafi kyau ga aikinmu na shimfida hanyar jirgin kasa, amma mu dakatar da aikinmu har cikin kwanaki 10 domin bar wadannan bareyi su bi ta gandun dajin nan lami lafiya. Da muka ga wata barewa irin ta Tibet ta ji rauni a kafarta, sai mun tafi da ita ofishinmu, mu wanke kafar da ta ji rauni da ruwan dumi, muka daura wa kafarta bandeji, muka ba ta madara. Bayan haka muka aika da ita zuwa wurin kare namun daji."

An ruwaito cewa, yawan kudi da aka kashe domin kare muhalli yayin da ake gudanar da aikin shimfida hanyar jirgin kasa da ke hada lardin Qinghai da jitar Tibet ta kasar Sin ya kai kudin Sin Yuan biliyan 1.4. Malam Dawaciren, shugban ofishin kula da harkokin birnin Lhasa na asusun kula da namun daji na duniya wato WWF ya nuna yabo ga hanyar da aka bi wajen kare muhalli. Ya ce, "bisa ma'aunin kare muhalli, aikin shimfida hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin wani aiki ne da aka yi ba tare da gurbata muhalli ba. Yayin da ake shimfida hanyar nan, an yi iyakacin kokari wajen kare muhalli."

Da wani jami'in ma'aikatar hanyar jirgin kasa ta Sin ya tabo magana a kan batun kare muhalli, bayan da aka fara aiki da wannan hanyar jirgin kasa, sai ya ce, za a dauki matakai iri daban daban wajen hana fasinjoji su zuba shara da ruwan dauda da makamantansu a waje daga cikin jirgin kasa don kare muhalli a wurare da hanyar jirgin kasa take. Ya kara da cewa, kasar Sin za ta yi kokari sosai wajen mayar da wannan hanyar jirgin kasa bisa matsayinta na hanyar jirgin kasa mai kare muhalli, ta yadda za a gwada misali dangane da kare muhalli yayin da ake gudanar da manyan ayyuka a kasar Sin. (Halilu)