Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-12 18:04:21    
Kara mai da hankali ga kula da harkokin shigi da fici da kasar Sin ta yi na da amfani ga kiyaye ire-iren naman daji

cri
Kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta bayar da ka'idojin Jamhuriyar Jama'ar Sin na kula da harkokin shigi da fici kan naman daji da tsire-tsiren daji wadanda suke kusan bacewa ta yadda za a kara kayadde aikin shigi da fici naman daji da tsire-tsire wadanda suke kusan bacewa. A lokacin da wata kwarariyyar hukumar yin nazari kan dabbobi ta cibiyar kimiyya ta kasar Sin kuma wakiliyar kungiyar yin nazari kan ilmin kiyaye abubuwa masu rai ko marasa rai na daji ta kasa da kasa da ke wakilci a kasar Sin Xie Yan ta karbi ziyarar da manema labaru suka yi mata, sai ta bayyana cewa, bayar da ka'idojin kula da harkokin shigi da fici kan naman daji da tsire-tsire shi ne aiki mai yakini da gwamnatin kasar Sin ta yi don ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar kasa da kasa ta kula da harkokin shigi da fici kan abubuwan da za su bacewa, wannan na da amfani ga kiyaye ire-iren abubuwan daji da kyau.

Bisa sabbin ka'idojin da aka bayar, an ce, kasar Sin ta hana dukan aikace-aikacen shigi da fici naman daji da tsire-tsire da za su fuskanci bacewa bisa makasudin kasuwanci da ciniki, ciki har da naman daji da tsire-tsire da kayayyakin da aka kera ta hanyar yin amfani da su wadanda ba a rada musu suna ko sabbi ne da aka gano su. A sa'I daya kuma, wajen yin binciken kimiyya da kiwonsu don kara ire-irensu da yin ma'amalar al'adu da dai sauransu, wato bukatar musamman da aka yi don shigi ko fici naman daji da tsire-tsiren daji , ana bukatar shigi da fici naman daji ko tsire-tsiren daji da suke fuskantar bacewa, dole ne a sami izni daga wajen sassa mai kula da harkokin naman daji da tsire-tsiren daji na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin bayan da hukumar kimiyya ta yi kimantawa a kansu. Kwarariyyar ofishin binciken naman daji da tsire-tsiren daji na cibiyar kimiyya ta kasar Sin Xie Yan ta bayyana cewa, a kasar Sin, game da ka'idojin nan, ya kamata a bayyana cewa, an kara zurfafa yarjejeniyar kasa da kasa ta kula da harkokin shigi da fici kan abubuwan da suke fuskantar bacewa. A da, a kasar Sin, ban da wadannan abubuwan, ba a kara karfin kiyaye sauran irinsu ba. Bayan da aka soma aiki da ka'idojin nan, manyan sassan kula da wadannan ayyuka su iya tsara wasu abubuwan halittu bisa halin da kasar Sin take ciki don kiyacye su . Saboda haka, yarjejeniyar nan ta kara karfin kasar Sin wajen aiwatar da harkokin nan.

Lokacin da ta tabo magana a kan amfanin da ka'idojin nan za su ba da wajen kiyaye abubuwan daji da suke fuskatar bacewa, Malama Xie ta bayyana cewa, ba za a iya samun izni da sauki ba wajen shigi da fici naman daji da tsire-tsiren daji da suke fuskantar bacewa bayan da aka aiwatar da ka'idojin nan . Da farko, dole ne hukumar kimiyya ta yi kimantawa ta hanyar kimiyya, sa'anan kuma za a sami izni daga wajen hukumomin kula da harkokinsu, ta hanyar ajandar nan, tabban ne za a hana wasu cinikayya da aka yi ba bisa kimiyya ba.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta riga ta zama daya daga cikin manyan kasuwannin shigi da fici naman daji da tsire-tsiren daji da kayayyakin da aka kera ta hanyar yin amfani da su a duniya. A shekarar 2005, yawan kudin da kasar Sin ta samu daga wajen ciniki na shigi da fici naman daji da tsire-tsiren daji ya kiai kudin Sin Yuan biliyan 140, ya karu da kashi 70 bisa na shekarar 2004. Saboda haka Malama Xie ta bayyana cewa, ana iya cewa, kasar Sin babbar kasa ce da ke yin amfani da naman daji da tsire-tsiren daji da yawa, a wani fanni, naman daji da tsire-tsiren daji da kasar Sin ta fita zuwa sauran kasashen waje na da yawan gaske, a wani fanni daban kuma, ta shigo da su da yawa daga sauran kasasshe, saboda haka, ya kamata a kayadde hakan da aka yi don rage mugun tasirin da aka kawo wa kasar Sin bisa sakamakon shigi da fici naman daji da tsire-tsiren daji da aka yi , wannan yana da ma'ana mai muhimmanci sosai.(Halima)