Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-06 17:56:54    
A yi yawon shakatawa a dutse mai suna Tai na kasar Sin

cri

Dutse da ake kira Tai cikin Sinanci yana lardin Shandong da ke a gabashin kasar Sin. Dutsen nan shahararren dutse ne na farko a duk kasar Sin gaba daya. A cikin ni'imataccen wuri na Dutsen Tai, akwai kololuwa da yawansu ya wuce 300, da rafuka sama da 260, da shahararrun tsoffafin bishiyoyi sama da dubu 20. Malam Yazima Haiuaki, dan yawon shakatwa da ya fito kasar Japan ya bayyana cewa, "dutsen Tai ya cancanci sunansa na dutse mafi shahara a kasar Sin. Mun yi matukar farain ciki da samun damar zuwa dutsen nan. Muhallinsa yana da kayatarwa, kuma shi tsohon wuri ne mai muhimmanci ga al'ummar Sin, haka zalika ya zama gada ne da ke hada zamanin da da yanzu. Bisa matsayinmu na baki 'yan kasashen waje mun yi farin ciki da ganin yadda aka kare shi sosai, domin yana tunatar da mu tarihi. "

Idan masu yawon shakatawa sun sami damar zuwa dutsen Tai musamman a yanayin bazara, to, za su more idonsu da bishiyoyi masu launin kore shar iri-iri masu ban sha'awa, za su shiga harkokin wasu bukukuwa da a kan shirya a yanayin bazara.

Lambun dashe-dashen bishiyoyi masu ba da wani irin 'ya'yan zaki da ake kira Cherry a Turance wani wuri ne mai kyau na ga masu yawon shakatawa musamman a yanayin bazara a dutsen Tai. Lambun nan yana arewacin kololuwa mai suna "Aolai' ta dutsen Tai. Yau sama da shekaru 100 da suka wuce, wani mutum mai suna Lu da 'ya'yansa maza sun shafe shekaru da yawa suna farfasa dutse, sun shimfida wani fili don dashe-dashen bishiyoyi masu ba da wani irin 'ya'yan zaki da ake kira Cherry a Turance. Daga wannan lokaci ne, bishiyoyin nan da aka dasa suka yi ta karuwa. Yanzu, bishiyoyin sun game ko ina cikin wannan kololuwar dutse. Yayin da masu yawon shakatawa ke hawa kan kololuwar, sun iya yada zango a lambun nan, su dandana 'ya'yan Cherry masu zaki, su ci abinci na gidajen manoma, to, tabbas ne, za su sha daularsu ainun.

Ban da wannan lambu, kuma akwai wani wuri da ya fi shahara wajen dashe-dashen bishiyoyi masu ba da wani irin 'ya'yan zaki daban da ake kira Peach a Turance. Sunan wurin nan shi ne Feicheng. Yau sama da shekaru 1000 da aka fara dashe-dashen irin wadannan bishiyoyi. Yanzu, fadin filayen bishiyoyin nan ya kai kadada 8000. Furanin bishiyoyin su kan tohu sosai a tsakanin watan Afrilu zuwa watan Mayu na ko wace shekara. Sabo da haka a kan iya more ido da furanin nan sosai a wannan lokaci. Malama Li Qing wadda ta dade tana zama a wurin nan ta bayyana cewa, "muna kiran wurinmu da sunan wurin furanni na dutsen Tai. Dalilin da ya sa haka shi ne domin a yanayin bazara furanni masu launin ruwan hoda na bishiyoyin Peach su kan game duk wurinmu. Idan wani ya sami damar zuwa wurinmu, to, zai ji dadi da more idonsa da wadannan furanni masu kyaun gani."

Ban da wadannan kuma, masu yawon shakatawa za su iya shiga wasu bukukuwa da a kan shirya don taya juna murna kamar "bikin baje koli na wurin ibada" da "bikin more ido da furannin bishiyoyin Peach" da sauransu. Malam Chen Feng, jami'in hukumar kula da harkokin yawon shakatawa na wurin ya bayyana cewa, "masu yawon shakatawa na kasashen waje da ke zuwa dutsen Tai sun yi ta karuwa a cikin shekarun nan da suka wuce. Yawancinsu sun fito ne daga Japan da Korea ta Kudu da Thailand da Singapore da Amurka da Canada da dai sauran kasashe. Nan gaba, za mu kara kokari wajen jawo masu yawon shakatawa na kasashen waje da su yi yawon shakatawa a dutsen Tai, ta yadda mutanen duniya za su kara fahimtar dutsen Tai." (Halilu)