Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-06 14:45:46    
Kasar Sin tana mai da hankali sosai a kan wakokin jama'a

cri

A 'yan shekarun baya, kasar Sin tana kara mai da hankali sosai a kan wakokin jama'a. A cikin gasar rera wakokin matasa ta kasar Sin da tashar CCTV ta shirya a shekarar bana, an yi gasar rera wakokin jama'a musamman, wadda ta fi jawo hankulan jama'a. Sai mu ga cikakken bayani a kan haka.

Tashar CCTV tana shirya wannan gasa ce a ko wane shekaru biyu, amma a cikin gasar da ta shirya a karo 11 da suka gabata, ba a yi gasar rera wakokin jama'a ba, amma a cikin gasar da ta shirya a shekarar bana, an yi wannan gasa a karo na farko.

Wakokin jama'a su ne hanyoyin wakoki daban daban da jama'a ta kabilu daban daban suke rera a cikin zaman rayuwarsu, wadannan wakokin jama'a suna gada daga zuriya zuwa zuriya a tsakanin manoma da makiyaya da mata da dai sauransu, su ma wani muhimmin sashe na abubuwan tarihi na al'adu da ake gada daga kakanni kakanni na kasar Sin. Ana rare wakokin jama'a ne ba tare da hora ba.

A cikin 'yan kwanakin baya, tare da bunkasuwar tattalin arziki da zamanintar da duniya cikin sauri, wakoki masu farin jini suna kara dora wani muhimmin tasiri a kan jama'a, a sakamakon haka, yawan mutanen da ke mai da hankali a kan wakokin jama'a ya ragu sosai. A cikin yankunan kananan kabilu da yawa, tsofaffi kawai suna rare wakokin jama'a, matasa ba su kaunar wakokin jama'a ba.

Game da haka, gwamnatocin daban daban na kasar Sin sun dauki matakai cikin yakini domin kara kare wakokin jama'a, haka kuma sun nuna goyon baya a kan aikin nazarin wakokin jama'a, da nufin kara yaduwar wakokin jama'a ta hanyoyi daban daban. A cikin wasu yankunan da kananan kabilu ke zama, an kadammar da aikin kare al'adun jama'a da dai sauransu. Bayan kokarin da duk zaman al'ummar kasar Sin suka yi tare, an fara farfado da wakokin jama'a.

Tashar CCTV ta shirya gasa rera wakokin jama'a a cikin gasar matasa, wannan yana da ma'ana sosai ga aikin kare abubuwan tarihi na al'adu da ake gada daga kakanni kakanni na kasar Sin. Wani mawaki 'dan kabilar Zang kuma alkalin wannan gasa Zongyongzuoma ya nuna yabo sosai a kan haka, yana ganin cewa, 'ta gasar da tashar CCTV ta shirya, matasa suna iya sanin da fahimtar kyawawan wakokin jama'a na kabilu 56 na kasar Sin, ina fata matasa za su kaunar su da sanin su da kuma rera su.'

Wannan gasar rera wakokin jama'a ta kabilu daban daban da a aka shirya ta jawo hankulan jama'a sosai. Game da mutane da ba su san wakokin jama'a sosai ba, wannan gasa ta zama wata kyakkyawar dama da su fahimci wakokin jama'a. Malama Chen da ke kallon gasar cikin jerin kwanaki ta bayyana cewa, 'wannan shi ne karo na farko da na saurari wakokin jama'a ta kabilu daban daban. A da na yi tsamani cewa, wakokin jama'a su ne wakokin da 'yan kananan kabilu suke rera a yayin da suke aikin gona, ba su da dadin ji. Amma da na kalli wannan gasa, ashe na san cewa, a da na yi kuskure, wakokin jama suna da dadin ji sosai.'

Wasu kwararrun da abin ya shafa sun bayyana cewa, ana mai da hankali sosai a kan wakokin jama'a, to, wannan yana da ma'ana sosai a kan aikin kare al'adun jama'a. Kungiyar kare al'adun jama'a ta kasar Sin ta taba baga waga ga wannan gasar da tashar CCTV ta shirya, inda ta ce, wannan gasa za ta taka wata muhimmiyar rawa a kan kare al'adun jama'a da kare abubuwan tarihi na al'adu da ake gada daga kaka da kakanni na kasar Sin.(Danladi)