Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-06 12:28:13    
Kasar Sin za ta gina wata kungiyar kwararrun kimiyya da fasaha masu iya kafa sababbin abubuwa cikin gaggawa

cri

Ran 5 ga wata a nan birnin Beijing, an shirya babban taron mambobin majalisar kimiyya da na cibiyar injiniyoyi na kasar Sin. A gun bikin bude taron, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi jawabi cewa, nan gaba kasar Sin za ta dauki matakai, kamar kyautatta sabon tsarin kafa sababbin abubuwan kimiyya da fasaha, da gyara tsarin zabi da horar da kwararrun kimiyya da fasaha, da dai sauransu, domin gina wata kungiyar kwararrun kimiyya da fasaha masu kafa sababbin abubuwa, da kuma nuna goyon baya sosai ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma wajen kimiyya da fasaha. Yanzu, ga bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana:

Majalisar kimiyya ta kasar Sin, da kuma cibiyar injiniyoyi ta kasar su ne manyan hukumomin ba da shawara wajen fannonin kimiyya da fasaha, da fasahar jinjiniyoyi, su ne kuma muhimman sansanin horar da kwararrun kimiyya da fasaha na kasar Sin. A gun bikin bude bababn taron mambobin majalisar kimiyya da na cibiyar injiniyoyi da aka shirya a ran 5 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayyana cewa, ya kamata a mai da ayyukan horar da kwararrun kimiyya da fasaha masu kafa sababbin abubuwa cikin gaggawa ta zama wata muhimmiyar manufar kasar, ya ce,"Horar da kwararrun kimiyya da fasaha masu kafa sababbin abubuwa mai dorewa cikin gaggawa, wannan ne bukatun da ke wajabta wajen kara karfin kafa sababbin abubuwa, da kuma kafa wata kasa mai kafa sababbin abubuwa, tilas ne mu tsaya kan wannan tsare-tsaren manufa, wato albarkatun kwararru shi ne albarkatun da ya fi muhimmanci, da kuma gina wata kungiyar kwararrun kimiyya da fasaha mai kafa sababbin abubuwa cikin gaggawa."



A cikin shekaru sama da 20 da suka wuce, sha'anin kimiyya da fasaha na kasar Sin ya samu bunkasuwa da sauri, amma shugaba Hu Jintao ya ce, bisa halin bunkasuwar kimiyya da fasaha ta duniya, bunkasuwar sha'anin kimiyya da fasaha na kasar Sin yana fuskantar kalubane mai tsanani:"An kasance da babban gibi a tsakanin matsayin kimiyya da fasaha na kasar Sin da na duniya, musamman kasar Sin ba ta da karfi sosai wajen kafa sababbin abubuwa, kuma lambobin kirkira ba su da yawa, wasu muhimman fasaha suna dogara da kasashen waje, kanana da manyan masana'antun kimiyya su ma ba su da yawa, kwararrun fannin nan ba su da yawa, kuma an kasance da matsaloli da yawa a cikin tsarin kimiyya da fasaha."

Yanzu, kasar Sin ta riga ta gano cewa, ba za a iya tabbatar da burin gina wata kasa mai kafa sababbin abubuwa ba, idan babu wata babbar kungiyar kwararrun kimiyya da fasaha. A gun babban taro, shugaba Hu Jintao ya bukaci bangarori daban daban da ke da nasaba na kasar Sin da su ci gaba da karfafa gyare-gyaren tsarin kimiyya da fasaha, ya ce,"Ya kamata a matakai daban daban, da hukumomin da ke da nasaba su ba da muhimmanci ga jagoranci, da ba da kuhiman taimako na kasuwa wajen kasafin albarkatu, da kuma kafa da kyautata tsarin horar da kwararru, da yin amfani da darajanta ga kwararru, da dai sauransu; da kyautatta tsarin ba da kwarin gwiwa ga masana'antu da su kara zuba jari kan fannin kimiyya da fasaha; da kuma kyautatta tsarin ikon mallakar ilmi."

Bayan haka kuma Mr. Hu Jintai ya bayyana cewa, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da kara ba da tarbiya don samu kwarewa gaba daya, da kara ayyukan yaduwar kimiyya. Baya ga haka kasar Sin za ta kara karfin shigar da kwararru.

Bisa labarin da muka samu an ce, za a shafe kwanaki 4 ana yin wannan babban taro.  (Bilkisu)