Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-29 16:50:11    
Kasar Sin tana kokarin aiwatar da yarjejeniyar duniya don hana shan taba

cri
Ran 29 ga wata, jami'in ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya bayyana a gun taron yada labaru da aka shirya a nan birnin Beijing cewa, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da "yarjejeniyar ka'idojin hana shan taba" a watan Janairu na shekarar nan, kasar Sin tana kokari sosai wajen kafa doka da yin farfaganda kan rage shan taba bisa ka'idojin yarjejeniyar.

"Yarjejeniyar ka'idojin hana shan taba" yarjejeniyar duniya ce ta farko da aka daddale a karkashin jagorancin hukumar kiwon lafiya ta duniya. Makasudinta shi ne don rage shan taba a duk duniya musammam ma a kasashe matasa. Kasashe sama da 100 ciki har da kasar Sin sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar nan daya bayan daya.

Malam Zhang Bin, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin kiwon lafiyar mata da kananan yara da wuraren zaman jama'a na ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya bayyana cewa, "tun bayan da aka fara aiwatar da yarjejeniyar ka'idojin hana shan taba ta hukumar kiwon lafiya ta duniya a kasar Sin a watan Janairu na shekarar nan, ka'idoji da dokokinmu da abin ya shafa ba su da kyau sosai, idan an kwatanta su da ka'idojin yarjejeniyar nan, sabili da haka yanzu muna kokari sosai wajen yin kwaskwarima a kan wadannan ka'idoji da dokoki don kyautata su."

Malam Zhang Bin ya gwada misali cewa, an kyautata ka'idojin hana shan taba a wuraren jama'a wadanda aka tanada a cikin gyararren daftarin dokokin kiwon lafiya a wuraren jama'a da aka gabatar wa majalisar gudanarwa ta kasar Sin don dudduba shi da kuma zartas da shi. Ban da wannan kuma dangane da dokokin talla da ake yi musu kwaskwarima, za a hana talla da wasu kamfanonin taba na kasar Sin ke yi a kan samfurorin tabarsu a habaice.

Haka zalika kasar Sin tana kara kokari wajen yin farfaganda a kan rage shan taba. A gabannin ran 31 ga wannan wata, wato ranar yaki da shan taba a duniya, ana ta yin farfaganda kan illar da shan taba ke kawo wa lafiyar jikunan mutane a wurare daban daban na kasar Sin. Kasar Sin ta kuma shirya gasar yaki da shan taba ta duniya ta shekarar 2006. Ya zuwa ran 1 ga wannan wata, yawan mutane da suka yi rajistar sunayensu don shiga cikin gasar ya wuce dubu 90 a kasar Sin. Yanzu, gasar nan ta zama irin wannan gasa mafi girma a kasar Sin.

A gun taron watsa labaru da aka shirya a ran 29 ga wata, hukumomi da abin ya shafa na kasar Sin sun bayar da rahoto a kan shan taba da kiwon lafiya a kasar Sin a shekarar nan. Babban jigon rahoton nan shi ne yaki da shan taba da shawo kan ciwon sankara. A cikin rahoton nan an shaida cewa, yawan mutane da ke kamuwa da cutar sankara da wadanda ke mutuwa a sakamakon shan taba yana karuwa da sauri a kasar Sin.

Kasar Sin kasa ce mafi girma wajen fitar da taba da shan taba a duniya. Yawan taba da ake yi da yawan mutane da ke shan taba a kasar Sin dukanninsu ya dauki sulusin na duk duniya. Sabo da haka aikin yaki da shan taba yana da muhimmanci a kasar Sin, sa'an nan kuma ana shan wahala wajen yinsa. Malam Zhang Bin, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin kiwon lafiyar mata da kananan yara da wuraren zaman jama'a na ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya ce, "yanzu, mun fara aiwatar da yarjejeniyar ka'idojin hana shan taba ba da dadewa ba, akwai matsaloli masu yawa da muke fuskanta. Yaki da shan taba ba ma kawai wata matsalar kiwon lafiya ce mai tsanani ta dogon lokaci ba, har ma wata matsalar zaman jama'a da ta tattalin arziki ce da ta shafi karin farashin taba da haraji da aikin hana tallar taba da sauransu." (Halilu)