Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-05 19:38:50    
Kasar Sin ta yi kokarin kyautata halin da manoman 'yan kodago suke cikin birane

cri

Yanzu da akwai manoma da yawansu ya kai kusan miliyan 200 wadanda suke aikin kodago cikin biraren kasar Sin, yawan masu aikin yi da wadannan manoma suka dauka a sana'o'in gine-gine da hakar ma'adinai da yin gyare-gyare ya kai fiye da kashi 60 bisa 100, sabo da haka sun riga sun zama muhimmin karfin da ba za a iya watsi da shi ba wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin. To, yaya halin da wadannan manoma suke ciki wajen aiki da zaman rayuwarsu cikin birane? Cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayani kan wannan matsala.

A wani filin gine-gine da ke yammacin birnin Beijing, wakilinmu ya gana da Mr. Chen Qiangsheng wanda ya zo nan birnin Beijing a 'yan kwanaki kawai. Mr. Cheng wanda yake da shekaru 38 da haihuwa ya zo ne daga wani wuri maras ci gaba wajen tattalin arziki na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Yana da 'ya'ya 2, daya dan makarantar sakandare ne, daya daban kuma yana da shekaru 4 kawai da haihuwa, matarsa kuma tana yin aikin gona a garinsa, babban nauyin ciyar da 'yan iyalin ya rataya ne bisa wuyan Mr. Chen wanda yake aikin kodago a sauran wurare. Mr. Chen yana fatan samun kudi da yawa a nan birnin Beijing, amma hakikanan abubuwan da ya gumu da su sun jawo masa karayar zuci. Ya ce, "An ba da ramammen albashi, wato kudin Sin Yuan 35 kawai nake samu a kowace rana. Sharudan wurin kwana kuma ba su da kyau."

Domin kyautata halin zaman manoma da suke aiki cikin birane, kwanan baya gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wata takardar kan "Wasu ra'ayoyi da aka dauka domin daidaita matsalolin manoma 'yan kodago", kuma ta shigar da matsalar manoma da suke aiki cikin birane cikin cikakken shirin raya kasa baki daya.

Mr. Hu Xiaoyi shi ne mataimakin ministan kodago da samun tabbaci ga zaman al'umman kasar Sin, kuma direktan ofishin hadadden taron ayyukan manoma 'yan kodago na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya dade yana ta mai da hankali kan matsalar manoma 'yan kodago. Ya bayyana cewa, idan an kwatanta wannan takarda da sauran takardun da aka bayar a da kan matsalolin manoman da suke aiki cikin birane, sai a iya gane cewa, abubuwan da aka rubuta cikin wannan takarda an tsai da su ne ta tsararriyar hanya kuma ta hanyar hengen nesa. Ya ce,

"Abubuwan da aka rubuta cikin takardar sun shafi duk fannoni kuma an tsai da su ne ta tsararriyar hanya. Takardar tana kunshe da batutuwa 40, daga cikin su kuma da akwai 32 wadanda aka tsai da su musamman domin daidaita hakikanan matsalolin manoma 'yan kodago daga fannoni daban-daban. Alal misali da akwai matsalolin dagantakar kodago, da albashin 'yan kodago da dakunan kwanansu da batun ba da ilmi ga 'ya'yansu da kuma kiwon lafiyarsu. An tsai da wadannan dokoki ne ta tsararriyar hanya kuma bisa harsashin manufofi da matakan da aka dauka a da, kuma an tsai da su ne bisa hangen nesa."

Wannan takarda ta zama wata takarda ce da ta mai da hankali sosai domin daidaita hakikanan matsalolin da manoma suke gamuwa da su a lokacin da suke aikin kodago cikin birane, sabo da haka wadannan manoma suna cike da imani sosai kan matsalar kyautata halin da suke ciki yanzu.