Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-26 15:12:23    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(20/04-26/04)

cri
Akwai labaru 2 da aka ruwaito mana game da wasannin Olympic na Beijing da za a yi a shekarar 2008. Don ci gaba da yin amfani da gine-ginen wasannin Olympic bayan gasa, za a sayar da gidajen da ke kauyen wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 ga al'ummar kasar Sin, bayan da aka kammala wasannin Olympic na nakasassu na shekarar 2008.

Ban da wannan kuma, mataimakin zaunannen babban sakataren kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasar Sin Mr. Zhao Sujing ya fayyace a kwanan baya cewa, za a kafa sansanin horar da 'yan wasa nakasassu na farko a nan Beijing a farkon shekara mai zuwa. Kungiyar wakilan 'yan wasa nakasassu ta kasar Sin za ta yi amfani da wannan sansani don share fage ga wasannin Olympic na nakasassu na Beijing. Bayan gasar, za a bude shi ga dukan nakasassu.

An yi gasar iya tafiya da sauri ta duniya da Hadaddiyar kungiyar wasan tsalle-tsalle da guje guje ta duniya wato IAAF ta shirya a birnin Yangzhou na lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin a ran 22 ga wata, 'yan wasan kasar Sin sun kwashe dukan lambobin zinare na gasar iya tafiya da sauri mai tsawon kilomita 20 na rukunonin maza da mata. Li Gaobo ya zama zakara da awa 1 da mintoci 18 da dakikoki 17 a tsakanin maza, He Dan ta zama zakara da awa 1 da mintoci 28 da dakikoki 20 a tsakanin mata.

Ran 22 zuwa ran 23 ga wata, a birnin Jakarta, hedkwatar kasar Indonesia, kungiyoyin kasashen Sin da Indonesia sun yi takara da juna don samun damar shiga gasar share fage ga rukuni na farko na gasar cin kofin Federations ta wasan kwallon tennis ta shekarar 2006. A karshe dai, kungiyar kasar Sin ta lashe ta kasar Indonesia da ci 4 da ba ko daya. Wannan maki ne mafi kyau da kungiyar wasan kwallon tennis ta mata ta kasar Sin ta samu a cikin wannan babbar gasar tsakanin kungiyoyin mata mafi nagarta a duk duniya.

Ran 22 ga wata, a birnin Moscow, hedkwatar kasar Rasha, an yi bikin jefa kuri'a cikin kungiya kungiya domin gasar fid da gwani ta wasan kwallon kafa ta mata matasa ta duniya ta shekarar 2006, an mayar da kungiyoyin kasashen Sin da Rasha da Jamus da kuma Amurka a matsayin gogaggun kungiyoyi na rukunoni 4. Za a yi wannan gasa a kasar Rasha tun daga ran 16 ga watan Agusta zuwa ran 6 ga watan Satumba na wannan shekara, kungiyoyi 16 za su shiga wannan gasa, yanzu kungiyoyi 14 sun riga sun sami damar shiga wannan gasa.(Tasallah)