Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-12 18:19:38    
Kasar Sin ta yi watsi da zancen iska da Amurka ta yi wai kasar Sin ta kasa karfin kiyaye ikon mallakar fasaha

cri
A gun taron manema labaru da ofishin ba da labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 11ga wata a nan birnin Beijing, an gayyaci manyan jami'an hukumomi 6 da su bayyana sabon ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kiyaye ikon mallakar fasaha. A gun taron jami'an sun yi watsi da zancen banza da Amurka ta yi kwanan baya dangane da manufofin da kasar Sin ta dauka kan ikon mallakar fasaha, kuma sun bayyana cewa kasar Sin tana rubanya kokari don kiyaye ikon mallakar fasaha, kuma ta dauki hakikanan matakai domin murkushe ayyukan laifuffukan da aka yi na kai hari kan ikon mallakar fasaha. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana kan wannan labari.

Tun farkon wannan shekara zuwa yanzu, kullum Amurka tana matsa wa kasar Sin lamba don bukatar ta da ta daidaita matsalar gibin cinikin da ake yi tsakanin kasashen 2. Kuma ta shafa wa kasar Sin kashin kaji kan batun ikon mallakar fasaha, Amurka kullum tana yin kururuwa cewa, danyun aikin da ake yi cikin kasar Sin wajen satar yin kofin fayafaye da manhaja da sauran kayayyaki kamar su redio da redio mai hoto sun haddasa hasarar biliyoyin dala ga masana'antun Amurka a kowace shekara. A ran 11 ga wata da safe agogon Amurka a birnin Washington, jami'an kasashen 2 wato Sin da Amurka sun yi shawarwarin shekara-shekara kan ciniki, batun ikon mallakar fasaha ya zama daya daga cikin muhimman batutuwan da aka yi shawarwari a kai tsakanin bangarorin 2.

Kan zancen banza da Amurka ta yi, kasar Sin ta mai da martani sosai daga birnin Beijing. Tun kafin wasu sa'o'in da fara shawarwarin tsakanin jami'an tattalin arziki da ciniki na kasashen 2, sassa 6 ciki har da ma'aikatar kasuwanci, da babbar hukumar masana'antu da kasuwanci, da hukumar kula da harkokin watsa labaru da madaba'u da kotun koli ta jama'ar kasar Sin sun yi taron manema labaru cikin hadin gwiwa, inda suka bayyana sabon ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kiyaye ikon mallakar fasaha.

A gun taron, Mr. Jiang Zengwei, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana nan tana kara rubanya kokari don kiyaye ikon mallakar fasaha, da kai farmarki kan laifuffukan hai hari kan ikon mallakar fasaha. Ya ce, "Kotunan sama da matakin tsaka-tsakiya na kasar Sin dukkansu sun kafa kotunan shari'a na musamman domin daidaita matsalolin da suka shafi ikon mallakar fasaha. Yawan matsalolin da kotunan kasar Sin suka daidaita a shekarar 2005 dangane da matsalar kai hari kan ikon mallakar fasaha ya kai 3567, wato ya karu da kashi 27.9 cikin 100 bisa na shekarar bariya. Wadannan hakikanan abubuwa sun ba da shaida sosai cewa, kasar Sin ta samu babbar nasara a fannin kiyaye ikon mallakar fasaha ta hanyar shari'a".

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana kuma, Bo Silai, ministan kasuwanci na kasar sin ya karyata zancen banza da aka yi cewar wai matsalolin ikon mallakar fasaha da ke kasancewa a kasar Sin sun zama muhimmin abun da ya jawo tasiri ga gibin kudin da aka samu wajen cinikin da ake yi tsakanin Amurka da Sin. Ya ce, "Cikin kayayyakin da Amurka ta fitar zuwa nan kasar Sin, kayayyakin  kimiyya da fasahar zamani kuma masu ikon mallakar fasaha sun yi kadan. Sabo da haka a ganina da a ce dalilin da ya samar da gibin kudin ciniki tsakanin Amurka da Sin sabo da matsalar ikon mallakar fasaha ce, gwamma a ce sabo da kayyadewar da Amurka ta yi wajen fitar da kayayyakin  kimiyya da fasahar zamani zuwa kasar Sin ne."