Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-05 12:40:53    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(03/30-04/05)

cri
......Kwanakin baya ba da dadewa ba, wani jami'in hukumar ba da jagoranci ga gine-ginen wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2008 da za a yi a Beijing ya fayyace, cewa wannan shekara, muhimmiyar shekara ce ta yin wannan mashashan aiki. Yanzu injiniyoyi da ma'akata da yawansu ya wuce 17,000 suna nan suna yin aiki ba ji ba gani. Kuma ana sa ran za a kammala ayyukan gina babban filin wasannin motsa jiki mai siffar tsuntsu na kasar Sin da kuma sauran gine-gine a daidai lokaci.

......Tun daga ran daya ga wannan wata ne aka soma yin kwaskwarimar gine-ginen cibiyar wasannin motsa jiki na Olympics na kasa na birnin Beijing domin wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2008. Za a kammala wannan aiki ne a watan Agusta na shekara mai zuwa.

......A ran 31 ga watan jiya, a nan birnin Beijing, kwamitin kula da harkokin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijig ya shelanta, cewa tun daga wannan rana ne aka soma karbar kalaman kirari na masu aikin sa kai daga duk duniya domin taron wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2008 da za a yi a nan Beijing. An jaddada, cewa ya kamata kalaman kirari su hada da hasashen cewa ' a mai da aikin hidima da shimfida zaman jituwa a gaban komai'. An kuma bayyana, cewa duk wadanda suke son rubuta kalaman kirari, za su iya gabatar da bayanansu ta gidan waya ko hanyar internet ; kuma za a iya samun takamaiman labarai game da wannan lamari a kan shafin internet ta kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing. Adireshin shafin, shi ne www.beijing 2008.com ;

......A ran 31 ga watan jiya, an yi wani gagarumin bikin kunne wutar yula na babban taron wasannin motsa jiki na 3 na duk kasar Sin a birnin Suzhou dake gabashin kasar, wanda kuma za a gudanar da shi daga ran 20 zuwa ran 30 ga watan gobe a birnin Suzhou. Ana sa ran akwai ' yan wasa kimanin 6,000 da za su halarci taron wasannin.

..... An kawo karshen gasar cin kofin duniya ta wasan mata na tseren gajeren zango a kan kankara tare da sa takalma dake daure da karfe a ran 2 ga watan nan a birnin Minneapolis na kasar Amurka. Kungiyar kasar Sin ta samu lambobin zinariya guda biyu. ' Yar wasa mai suna Wang Mong ta zama lambawan a gun gasar tseren mita 500 kan kankara ; kuma kungiyar mata ta samu lambar zinariya a gun irin wannan wasa na yada kanin wani.( Sani Wang )