Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-04 17:07:09    
Kasar Sin tana nazarin allurar rigakafin annobar murar tsuntsaye domin dan Adam

cri

A halin yanzu dai, annobar murar tsuntsaye tana yaduwa a ko ina a duk duniya. Ba ma kawai tana kashe tsuntsaye ba, har ma ta jawo barazana ga lafiyar dan Adam. Saboda ya zuwa yanzu ba a sami wani maganin da zai iya shawo kan wannan mummunar annoba ba, saboda haka, ba yadda za su yi, sai dai mutane sun yi allurar rigakafi don kare kansu. Yanzu kasar Sin tana nazarin allurar rigakafin annobar murar tsunstaye domin dan Adam. A cikin shirinmu na yau na 'kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya', za mu gabatar muku da halin da kasar Sin take ciki a wannan fanni.

A shekaru 2 da suka wuce, annobar murar tsuntsaye ta bullo a wasu yankunan kasar Sin, amma abin farin ciki shi ne babu mutumin da ya kamu da wannan ciwo. A cikin irin wannan hali ne, nan take gwamnati da hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin sun gane barazanar da wannan mummunar annoba ta kawo wa mutane, shi ya sa, nan take suka himmantu kan nazarin allurar rigakafin annobar murar tsuntsaye domin dan Adam.

Kamfanin fasahar ilmin halittu na SINOVAC na kasar Sin kamfani ne na farko da ya fara nazarin allurar rigakafin annobar murar tsuntsaye domin dan Adam. Bayan da ya ci nasarar jarraba allurar rigakafin da ya yi nazari a kai a kan beraye, kamfanin nan ya samar da allurar rigakafi don yin jarrabawa kan mutane.

Ran 16 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, bayan da hukumar sa ido kan abinci da magunguna ta kasar Sin ya kimanta allurar rigakafin da ya samar da ita, kamfanin SINOVAC ta sami izinin jarraba wannan allurar rigakafi kan mutane. Amma a ran nan, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta sanar da cewa, wani mutum ya kamu da annobar murar tsuntsaye. Saboda haka, nan da nan kamfanin SINOVAC ya kyautata jarrabawarsa, yana fatan za a yi jarrabawa a kan mutane tun da wuri. Jin kadan, kungiyar jarrabawar da kamfanin SINOVAC da asibitin sada zummunta tsakanin Sin da Japan na Beijing suka kafa sun tattara masu aikin sa kai don yin jarrabawa. Darektan sashen kula da ciwace-ciwacen numfashi na asibitin nan na Beijing kuma babban jami'in kula da yin jarrabawa kan dam Adam Mr. Jiangtao ya bayyana cewa, masu aikin sa kai sun amsa kirar da aka yi cikin himma da kwazo, wannan ya ba shi mamaki sosai. Ya ce, 'masu aikin sa kai sun zo ne daga rukunoni daban daban, kamar su likitoci da nas-nas da ma'aikatan kamfanoni da 'yan kwadago manoma. Duk sunayensu sun yi rajista, don a yi musu jarrabawar nan, abu ne mamaki kwarai da gaske.'

An zabi masu aikin sa kai 6 da suka fi dacewa da aka yi musu jarrabawa. Ran 22 ga watan Disamba na shekarar 2005, allurar rigakafi ta shiga jikin wadannan masu aikin sa kai na rukuni na farko.

Malama Zhang, wata nas ce mai shekaru 20 da haihuwa, ko da yake tana da wasu ilmin likitanci, amma bayan da aka yi mata allurar rigakafi, ta nuna dan damuwa kadan. Ta ce, 'bayan da aka yi mini allura, ina jin damuwa kadan, ina shakkar ko in kamu da zazzabi ko a'a, amma a zahiri kuma, ba wani abu da ya taba ni ba.'

Kamar yadda malama Zhang take, masu aikin sa kai na rukuni na farko ba su sami wata matsala ba, sun iya kare kansu saboda allurar rigakafi. An yi ta kara yin jarrabawa, ya zuwa yanzu, masu aikin sa kai fiye da 120 ba su sami wata matsala ba, an sami sakamako mai kyau.

Jami'in kula da samar da allurar rigakafin annobar murar tsuntsaye na ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Mr. Jia Jingdun ya yi bayanin cewa, ko da yake za a kammala jarrabawa ta mataki na farko a watan Mayu ko watan Yuni na wannan shekara, daga baya za a ci gaba da yin jarrabawa na mataki na biyu da na uku, har zuwa na hudu, amma ya yi limani da nazari da ake yi wajen samar da allurar rigakafin annobar murar tsuntsaye domin dan Adam. Ya ce, 'yanzu allurar rigakafin da muka yi nazari a kai za ta iya kiyaye dan Adam. An tabbatar da ita kan jikin mutane, za a zurfafa nazari, amma na yi limani da cewa, allurar rigakafi tana da amfani, an ba ta tabbaci a fuskar fasaha.'

Mr. Jia ya kara da cewa, ya zuwa yanzu akwai sauran rina a kaba wajen sayar da allurar rigakafin annobar murar tsuntsaye domin dan Adam ga al'ummar kasar, amma kasar Sin ta riga ta share fage cikin himma da kwazo. Yanzu an riga an shirya na'urorin samar da allurar rigakafin nan, bayan da aka kammala duka jarrabawa a kan mutane, ko kuma wani abu ya faru ba zato ba tsammani, bayan da hukumomin kasar da abin ya shafa suka yarda, za a samar da wannan allurar rigakafi nan da nan.(Tasallah)