Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-04 09:43:26    
Kasashen da ke yankin Sahel sun fara shirin raya "babbar ganuwa mai launin kore"

cri
Assalamu alaikum, jama'a masu karatu. Barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na "Afirka a Yau". A ran 30 ga wata a birnin Dakar, wato babban birnin kasar Senegal an rufe taron tattaunawa kan yadda za a kare muhallin yankin Sahel. Kasashen Senegal da Mauritania da Mali da Nijeriya da Togo da Chadi da Burkina Faso ne suka shirya wannan taro tare. A gun taron, an tsai da kudurin cewa, kasashen da ke yankin Sahel za su fara shirin "raya babbar ganuwa mai launin kore" wato za su fara shirin dasa itatuwa da ciyayi wanda aka dade an tsara wannan shiri.

Yankin Sahel yana kunshe da yankunan da ke tsakanin kudancin hamada na Sahara da filin ciyayi da ke arewacin kasar Sudan, fadin wannan ziri zai kai tsakanin kilomita 320 da kilomita 480. A wannan ziri, a kan yi ruwan sama kadan. Yanzu, ana son dasa itatuwa a wannan ziri, da kuma raya wata babbar ganuwa ta kore domin hana hamada na Sahara, kuma hana yankunan da ke kusa da ziri da su zama sabbin wuraren hamada. Yau da wasu shekarun da suka wuce ne shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya ya gabatar da wannan shiri. Bisa wannan shiri, za a raya wani zirin itatuwa, wato fadinsa zai kai kilomita 5 da kuma tsawonsa zai kai kilomita dubu 7. Wannan ziri zai tashi daga kasar Senegal da ke yammacin Afirka, kuma zai ketare kasashen Mali da Jamhuriyar Niger da Chadi da Sudan da Habasha har zuwa kasar Djibouti da ke gabashin Afirka. A watan Yuli na shekarar bara, wakilan kasashe 23 na kungiyar hada kan kasashen da ke yankin Sahara-Sahel sun zartas da wani kuduri a birnin Dakar na kasar Senegal, inda suka yi bincike da duba kan wannan shiri ta hanyar kimiyya daga duk fannoni.

A gun bikin rufe taron tattaunawa kan yadda za a kare muhallin yankin Sahel, an kuma tsai da kudurin cewa, za a kafa hukumar daidaita ayyukan gina dam da raya babbar ganuwa mai launin kore a kowace kasar da abin ya shafa, kuma za a kafa wani rukunin kwararru domin duba halin ruwa da yanayi da ilmin halittu da ake ciki a wadannan kasashe. A sa'i daya kuma, za a fara zaben ire-iren itatuwan da za su dace da yanayin wadannan kasashe.

A gun taron, shugaba Abdoulaye Wade na kasar Senegal ya ce, muhimmin abun da ya kamata a mai da hankali shi ne ko za a iya yin amfani da ruwan da ke fuskar duniya kuma da ke karkashin kasa sosai. Mr. Wade ya yi kira ga kasashen da ke yankin Sahel da su yi kokari su gina dam da tafki domin tara ruwan sama da sauran ruwan da ke fuskar duniya. Sakamakon haka, za a yi amfani da wadannan ruwa domin dasa itatuwa da yin ban ruwa ga gonaki.

Bisa nazarin da kwararru suka yi, an ce, yau da shekaru fiye da dubu 10, yankin Sahel yanki ne da ke cike da ruwa da ciyaye tare da dabbobi iri iri da yawa. Amma domin sauye-sauyen yanayi da aikace-aikacen da dan Adam suka yi, yanzu wannan yankin Sahel ya zama wurin da ke da hamada kawai. Yankin Sahel ya kuma zama wuri mafi talauta a duk fadin duniya. Amma, a karkashin wannan yanki, an gano cewa, maadannanun man fetur sun kai ton biliyan 9.9 tare da man gas da ya kai fadincubicmita biliyan dubu 5. Sannan kuma akwai makamashin karfe da tagulla da uranium da dai sauran makamashin halittu iri iri. Bugu da kari kuma, yawan ruwan da ke karkashin yankin Sahara ya kai cubicmita biliyan dubu dari 3. Sabo da haka, a kan ce yankin Sahel yana da makoma mai haske sosai.

Kamar yadda Mr. Wade ya fadi, bayan kafuwar wannan "babbar ganuwa ta kore" a yankin Sahel, ba ma kawai zai kyautata yanayin daukan sauti ba ne, har ma za a sauya hanyar zamantakewar jama'a da ke da zama a yanki kwata kwata. A sa'i daya kuma, ko shakka babu, za a iya ciyar da tattalin arziki da zaman al'umma na yanki gaba. (Sanusi Chen)