Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-03 16:00:43    
Sinawa sun kara mai da hankali kan tsimi da kiyaye muhalli

cri

Yanzu, a nan kasar Sin a kai a kai ne ake dacewa da katsewar wutar lantarki da rufe famfon ruwa a gida ko a ofis da ake bukata, kuma ba a jefa bawon 'ya'yan itatuwa da takardu, kuma a kera da yi amfani da kayayyakin da suke tsimin yin makamashin halitta. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, lokacin da ake samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri, an bata makamashin halittu da kazamtar da muhalli sosai. Sinawa sun fara sanin cewa, yin tsimin yin amfani da makamashin halittu da kiyaye muhalli, wadannan muhimman matakai ne ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin hali mai dorewa. Sun kuma fahimci cewa, wadannan matakai za su yi kyakkyawan tasiri ga zamantakewarsu.

Mr. Ding Guopei, ya taba tattara bololi a garin Taizhou na lardin Zhejiang da ke kudu maso gabashin kasar Sin. A cikin shekaru 2 da suka wuce, aikinsa ya samu ci gaba cikin sauri. Ya kuma kafa wata masana'antar sake sarrafa aluminium da aka yi watsi da su. Ban da kudin da ya samu daga wajen wannan aiki, a kowace shekera ya iya samun sauran kudaden da suka kai kudin Renminbi yuan miliyan 3 domin sake yin amfani da gas da ya bullo lokacin da ake sarrafa aluminium. "Yanzu na gane, idan kana da hanya daidai, gas da aka yi watsi da shi za a iya yin amfani da shi."

An bayyana cewa, yanzu lardin Zhejiang ya riga ya zama wani muhimmin wurin da yake sake yin amfani da karfe da takardu da kayan plastic da kayan glass da aka zubar. Yawan kudaden jarin bola da aka samu a lardin ya kai kudin Renminbi yuan biliyan 45 a kowace shekara.

Sannan kuma, wasu masana'antun zamanin yanzu suna kuma mai da hankali kwarai kan yadda za a yi amfani da fasahohin zamanin yanzu wajen kyautata sana'o'in gargajiya domin rage yin amfani da makamashin halitta.

Yin tsimin makamashi da albarkatun halittu da kara mai da hankali kan kiyaye muhalli, yanzu sun riga sun zama muhimman ayyukan da gwamnatin kasar Sin ke yi. Kwanan baya, a gun wani taron da aka yi kan yadda za a raya makamashin halittu, Mr. Zeng Peiyan, mataimakin firayin ministan kasar Sin ya ce, yin tsimin yin amfani da makamashin halittu da kiyaye muhalli ya riga ya zama wata muhimmiyar manufar da kasar Sin ke dauka.

"A gaban sabon halin da ake ciki yanzu, a bayyane ne muka dauki matakin sauya hanyar neman bunkasuwar tattalin arzikinmu, wato za mu kara mai da hankali kan yadda za a raya tattalin arziki daga duk fannoni kuma cikin hali mai dorewa."

Yanzu gwamnatin kasar Sin ta riga ta fara aikin rage yin amfani da makamashin halittu da kiyaye muhalli. Haka nan kuma tana kokarin hada kan wadannan ayyuka biyu tare.

Jihar Tibet tana tudun Qingzang da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Wannan wuri ne mafi tsayi a duk duniya. Ana da isashen hasken rana, kuma jihar Tibet tana da wadatattun makamashin hasken rana. Yanzu a jihar Tibet, a wurare da yawa, za ka iya ganin naurorin yin amfani da karfin hasken rana. Basanciren, wani manomi ne na jihar Tibet. Ya gaya wa wakilinmu cewa, bayan ya samu wutar lantarki da aka samu daga wajen karfin hasken rana a gidansa, shi da iyalansa suna jin dadin zamantakewarsu. Basanciren ya ce, "Bayan an gina tashar samar da lantarki ta hanyar yin amfani da karfin hasken rana a kauye a shekara ta 2002, mun iya kallo shirye-shiryen TV da na VCD. Gidaje da yawa na kauyenmu suna yin amfani da TV da sauran naurorin lantarki da muke bukata."

A jihar Tibet, ba ma kawai ana yin amfani da karfin hasken rana domin samar da wutar lantarki ba, har ma ana yin amfani da shi domin yin wanka da dafa abinci da dai sauransu. A yi amfani da karfin hasken rana a jihar Tibet, ba ma kawai wannan yana kyautata zamantakewar manoma ba, har ma yana ba da gudummawa wajen kiyaye muhallin tudun Qingzang.

Bugu da kari kuma, yanzu wuare da yawa ciki har da jihar Xingjiang da jihar Mongolia ta gida, ana yin amfani da karfin hasken rana da karfin iska domin samar da wutar lantarki da ake bukata. A wasu wuraren da suke da nisa da manyan birane, an gina kananan dam na samar da wutar lantarki. Mutanen da suke zama a wadannan wurare sun yi amfani da karfin ruwa wajen dafa abinci da dimame ruwa. An bayyana cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta kara karfin yin amfani da makamashin halittu da zai iya sake bullowa. Masana wadanda suka kware kan ilmin tattalin arziki ma suna mai da hankali kan yadda za a yi tsimin yin amfani da makamashin halittu da maganar kiyaye muhalli. Ana fatan gwamnatin kasar Sin za ta kara tsara jerin manufofi domin nuna goyon baya ga yunkurin nan. (Sanusi Chen)