Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-02-21 10:15:18    
Kwamitin shirya wasannin Olimpic na birnin Beijing ya kai ziyara ga Torino, domin koyon fasahohi masu kyau na wasannin Olimpic na lokacin dari na Torino

cri
Bayan da aka rufe wasannin Olimpic na lokacin dari na Torino na karo na 20 da aka shirya a watan Feburairu na shekarar da muke ciki, wasannin Olimpic na lokacin bazara na karo na 29 da za a kira a shekarar 2008 a nan birnin Beijing ya zama ainihin muhimmin abu da ke jawo hankulan dukan duniya. Wannan karo na farko ne da birnin Beijing ya daukan nauyin babban wasa na duniya kamar haka, wannan kuma babbar jarrabawa ne ga mutanen kasar Sin. Domin shirya wasan Olimpic na shekarar 2008 mai kyau, bayan da birnin Beijing ya samun damar daukan nauyin wasan Olimpic a shekarar 2001, a ko wane wasannin Olimpic na lokacin bazara da na dari, kwamitin shirya wasan Olimpic na Beijing zai aika da kungiyoyin yin rangadin aiki masu yawan mutane, kuma ya yi haka a wannan wasan Olimpic na lokaci dari na Torino. Yanzu ga labari game da wannan da wakiliyarmu ta ruwaito mana:

Bayan da aka rufe wasan Olimpic na lokacin dari na Torino, akwai sauran shekaru 2 da rabi ke nan kafin a bude wasan Olimpic na Beijing. Masu shirya wannan wasan Olimpic suna fuskantar babban kalubale, to mene ne kalubalen da ya fi girma da suke fuskantar? Mr. Jiang Xiaoyu, mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin shirya wasan Olimpic na Beijing ya ce, "A ganina kalubalen da ya fi girma shi ne rashin fasahohi, sabo da ba mu taba daukan nauyin babban wasan duniya kamar haka ba, haka kuma muna da bukatun koyon wannan sosai."

Kuma ya kamata Beijing ya koyi fasahohi daga biranen da suka taba shirya ko suka shirya wasan Olimpic. Ko da ya ke wasan Olimpic na Toridom, shi ne wasan Olimpic na lokacin dari, amma wasan Olimpic na lokacin dari da na lokacin bazara ba su da bambanci sosai wajen shirya gasa. Sabo da haka, kwamitin shirya Olimpic na Beijing ya aika da manyan kungiyoyi zuwa Torino don yin rangadin aiki. Mr. Wangwei, wani mataimakin shugaban zartaswa daban na kwamitin shirya Olimpic na Beijing ya bayyana cewa, "Mun raba kwamitinmu zuwa kashi biyu, yawanmu ya kai fiye da 200, domin koyi fasahohi daga wasan Olimpic na Torino, wani sashe ya koyi bikin bude wasan, wani sashe daban kuma ya koyi bikin rufe wasa. Bayan haka kuma, kwamitin shirya Olimpic na Beijing ya aika da wasu mutanen da ake horar da su fiye da goma a wasu hukumomin da abin ya shafa a Torino."

Ko masu aiki na kwamitin shirya Olimpic na Beijing da suka yin rangadin aiki, ko mutanen da ake horar da su a hukumar hidima na kafofin watsa labaru, da ta fasaha, da ta hidimar masu taimako, da kuma sauran hukumomi, dukansu suna koyon fasahohin Torino, suna fata za su yi amfani da su a cikin ayyukan shirya wasan Olimpic na Beijing. Mr. Wangwei yana ganin cewa, wasan Olimpic na Beijing ya koyi fasahoyi masu kyau daga Olimpic na lokacin dari na Torino kan mahalli, da tsarin filayen gasa, da shirya sufuri, da dai sauransu.

Mr. Wangwei ya ce, "an shirya wasan Olimpic na lokacin dari na Torino da kyau, yana da muhimmancin musamma wajen shirya wasan, haka kamar takensa na 'PASSION LIVES HERE', ya bayar da alama mai zurfi gare mu, muna tsamani za mu ci gaba da koyi abubuwa da yawa." (Bilkisu)