Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-26 20:01:15    
Kunun da ake ci a gun bikin Laba

cri

A ran 7 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, ran 8 ga watan Disamba ne bisa kalandar gargajiya na kasar Sin. A kasar Sin, akan kira watan Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin da sunan watan La, kuma kalmar "8" ta zama "Ba" ke nan, shi ya sa ran 8 ga watan Disamba na kalandar gargajiya ta kasar Sin bikin Laba ke nan. Bikin Laba bikin gargajiya ne na al'ummmar kabilar Han ta kasar Sin, kuma ya zama kamar kidan farko ne na bikin bazara wato sabuwar shekara bisa kalantar kasar Sin. A gun bikin Laba akan sha wani irin kunu mai dadi sosai da ake kira kunun Laba. To, jama'a masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayani game da kunun Laba.

Tarihin shan kunun Laba da Sinawa ke yi yana da shekaru fiye da 1000. An fara bin wannan al'ada daga daular Song. A wannan zamani, a ran 8 ga Disamba na kowace shekara bisa kalandar kasar Sin, ko fadar sarkin kasa, ko kuma fadar gwamnati da haikali dukkansu suna dama kunun Laba. A tsakanin jama'a kuma, iyalai daban-daban su ma sukan dama kunun Laba domin ba da sadaka ga kakanin-kakani. Sa'an nan kuma duk 'yan iyali sukan hadu su sha kunun, kuma sukan ba wa dangogi da aminai kyautar kunun.

Akwai ire-iren kunun Laba da yawa. Bisa al'adar gargajiya da ake bi tsakanin jama'a an ce, cikin kunun Laba akwai muhimman abubuwa iri 8 da kayan zaki iri 8, dalilin da ya sa aka yi haka shi ne, sabo da cikin Sinanci kalmar "Ba" wato takwas tana da ma'anar "alheri". Muhimman abubuwan da ake amfani da su domin dama kunun su ne wake da shinkafa, cikin waken da ake amfani da su kuma har da jan wake da koren wake da dogon wake da waken soya da sauran wake iri-iri. Ire-iren shinkafa da ake amfani da su kuma su ne, gero da shinkafa da shinkafa da aka gyara ta sosai, da shinkafa mai yauki, da 'ya'yan wani irin ciyayi, da alkama da sha'ir da masara da dawa da sauran shinkafa iri-iri. Mai gida yakan iya zaben wasu irin shinkafa da wake da yake so daga cikinsu.

Kayan zaki da ake amfani da su domin dafa kunun Laba wadanda kuma akan zaba daga cikin 'ya'yan itatuwa masu zaki da aka adana da wasu ire-iren 'ya'yan itatuwan da ake kira walnut da Chestnut da hazel da Pine nut wadanda bawonsu ke da kauri, da markadadden dabino, da kwayoyin bi rana, da 'ya'yan bado, da gyada da gujiya da zabiba.

Bayan da aka shirya muhimman abubuwa da kayan zaki, sai a dafa su tare da ruwa cikin wata irin tukunyar fadi-ka-mutu kan murhun da aka kunna wuta kadan. Daga baya kuma a sa kayan zaki kamar sukari da rose da furen Osmanthus a ciki.

Idan wasu iyalai wadanda suka mai da muhimmanci wajen abinci, kuma sukan mai da hankali wajen launin kunun Laba sosai, wato ba su yi amfani da wake wadanda launinsu masu duhu ba, maimakon haka sukan dauki shinkafa mai yauki da kwayoyin hatsi da wani abu kamar bado da ke cikin ruwa, da 'ya'yan bado kawai, irin kunun da suka dama da irin wannan shinkafa fari ne fat kuma garau yake wato kamar madubi, an kwashe shi cikin kasaken cin abinci masu kyau, lalle yana da kyaun gani kuma da dadin ci. Ana iya cewa, cikin watan Disamba, ana sanyi kwarai har ma ga dusar kankara da ake yi, 'yan iyali daya sun zauna a kewayen tebur suna cin abinci, wato suna shan kunun Laba mai kamshi kuma mai zaki, lalle wannan ya zama wani al'amari mai kyau kuma mai dadi sosai. (Umaru)