Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-11 18:01:28    
Kasar Sin za ta kara bunkasuwar ilmin sana'a da kuma horar kwararrun 'yan kwadago cikin gaggawa

cri
Yanzu, matsalar kwarancin kwararrun ma'aikata a bakin aiki ta yi tsanani sosai a kasar Sin, wannan matsala ta riga ta kawo babban tasiri ga kyautata tsarin masana'antu, sabo da haka ta jawo hankulan kososhin gwamnati sosai. A gun taron aikin koyar da sana'ar na kasar Sin da aka yi a ran 7 ga wata, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya nuna cewa, nan gaba kasar Sin zata dauki matakai da yawa domin bunkasa ilmin sana'ar, da kuma horar da kwararrun 'yan gwadago masu yawa. Yanzu, ga cikakken labarin da wakiliyarmu ta ruwaito mana:

A kasar Sin, yawan kwararrun leburori ya kai kashi 1 cikin 3 bisa jimlar yawan lebur, amma masu gyara (technician) da manyan masu gyara sun kai kashi 4 cikin dari kawai. A wasu shiyyoyin da ke gabashin kasar, rashin kwararrun leburori ya riga ya zama wani muhimmin dalilin da ke hana kara ci gaban masana'antu. Dalilai su ne, bisa ra'ayin gargajiya na mutanen kasar Sin, ba su son zama leburori masu fasaha, suna tsammani, matsayin sana'ar kamar irin nan ya yi kasa da na sauran sana'o'i. Bayan haka kuma, ba a yi aikin koyar da sana'a sosai ba, wannan ma wani dalili ne da ke jawo wannan matsala.

A taron aikin koyar da sana'ar na kasar Sin da aka yi a ran 7 ga wata, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya nuna cewa, nan gaba za a mai da ilmin sana'ar kamar daidai da ilmi na yau da kullum, da ilmi bisa babban matsayi, kuma za a kara karfin bunkasa ilmin sana'a. Ya ce, "Ba ma kawai sana'o'I dabam daban na tattalin arzikin kasa na bukatar 'yan kimiyya, da injiniyoyi, da kuma kwararru masu kula da sana'o'i ba, har ma suna bukatar sauran kwararru dubu dubai, da leburori masu inganci miliyan darurruka. Idan ba a iya samun irin wadannan kwararru masu dimbin yawa ba, to, da kyar za a yin amfani da kayayyakin aiki kamar injuna iri na zamani sosai wajen fita da kayayyaki."

A hakika dai, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, gwamnatin kasar Sin da hukumomin aikin koyarwa suna ta kokarin samar da bunkasuwar ilmin sana'a, makarantar ba da ilmin sana'a na shiyyoyi dabam daban su kuma suna sa himma kan neman yadda ake bunkasa ilmin sana'a. Kamar misali: a jihar Hubei da ke tsakiyar kasar Sin, a shekarar da muke ciki, gwamnatin ta biya kudin Sin yuan miliyan 11 ga wadanda ke karatu a sakandare da yawansu ya kai dubu 10, domin samun ilmin sana'a na shekaru 1 zuwa 2.

Jihar Tibet da ke kudu maso yammancin kasar Sin tana sa himma kan bunkasuwar aikin ilmin sana'a. A da, jihar Tibet ta mai da hankali kan aikin ba da ilmi na yau da kullum, amma yanzu ilmin sana'a ya kara jawo hankulan mutane a kwana a tashi, kuma kudin da aka zuba a kai ya yi ta karuwa a ko wace shekara.

A taron aikin ba da ilmin sana'ar na kasar Sin da aka yi a ran 7 ga wata, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya bayyana cewa, nan gaba za a yi gyare-gyare kan tsarin kafa makaranta na ilmin sana'a na kasar Sin, za a dauki tsari na kasa, da na jama'a, kuma a cikin karkashin shugabancin gwamnati, bayan haka kuma gwamnatin za ta kara zuba jari, domin inganci bunkasuwar ilmin sana'a.

Bisa sabon takiti na bunkasuwar aikin koyar da sana'a, a yanzu da kuma wasu lokufa nan gaba, abiu mai muhimmanci na ilmin sana'a na kasar Sin shi ne horar da mutane masu neman aikin yi, da kuma mutanen masu aiki fasahar sana'a. (Bilkisu)