
Shugaban kwamitin harkokin zabe na kasar Liberia madam Frances Johnson-Morris ta ba da wata sanarwa a birnin Monrovia, hedkwatar kasar a ran 17 ga wata cewa, saboda babu wani dan takara da ya sami kuri'un da yawansu ya kai kashi 50 bisa dari a cikin zagaye na farko na babban zaben shugaban kasar, shi ya sa za a sake kada kuri'a na zagaye na 2 a kasar a ran 8 ga watan Nuwamba.
Madam Johnson-Morris ta bayyana cewa, bisa kididdigar da aka yi a yanzu, a cikin kuri'un da aka jefa cikin tasoshin jefa kuri'a da yawansu ya kai kashi 90 bisa dari, Mr. George Weah ya sami kuri'un da yawansu ya kai kashi 28.9 bisa dari, tsohuwar ministar kudi ta kasar madam Ellen Johnson-Sirleaf ta sami kuri'un da yawansu ya kai 19.7 bisa dari, za su shiga kada kuri'a na zagaye na 2.(Tasallah)
|