
A ran 4 ga wata, mataimakin shugaban kwamitin kungiyar EU Franco Frattini ya bayyana cewa, kungiyar EU za ta aika da kwararru zuwa kasar Morocco domin ba da taimako a kan aikin warware matsalar haramtattun 'yan kaka gida wadanda suka nemi shiga cikin yankin kungiyar EU.
A gun wani taron watsa labaru da aka shirya a birnin Brussels, Malam Frattini ya ce, bias bukatar da gwamnatin kasar Spain ta yi mata, kungiyar EU za ta aika da kwararru zuwa kasar Morocco domin ba da taimako ga kasar wajen saffara iyakar kasar da yi shirin ba da taimakon kudi ga kasar domin warware matsalar. Domin mayar da martani ga matakin da kungiyar EU ta dauka, ya kamata kasar Morocco ta koma dukkan haramtattun 'yan kaka gida wadanda suka shiga cikin yankin kungiyar EU.(Danladi)
|