A ran 20 ga wata hukumar tsara shirin samar da abinci ta kasa da kasa ta yi kira ga kasashen duniya da su samar wa kasar Angola taimakon kudin dolar Amurka kimanin miliyan 30 domin ba da taimako ga yaran kasar da ke fuskantar yunwa da ciwace-ciwace iri iri.
A wannan rana, hukumar tsara shirin samar da abinci ta kasa da kasa ta bayyana cewa, domin hukumar ba ta da isashen kudi, kuma babu sauran hanyar da za ta iya zaba, sai ta rage yawan kudaden da take samar wa kasar Angola.
Yanzu, hukumar tana aiwatar da shirin samar da abinci ga yara dubu dari 4 wadanda suke zaune a kudu maso yammancin kasar Angola. Amma yanzu hukumar tana bukatar dalar Amurka kimanin miliyan 30 cikin gaggawa ta yadda za ta iya ci gaba da aiwatar da shirin nan har karshen shekara mai zuwa. (Sanusi Chen)
|