
A ran 14 ga wata,shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da shugaban kasar Zambiya Levy M Wanawasa a hedkwatar majalisar dinkin duniya dake birnin New York na kasar Amurka.
Mr.Hu Jintao ya ce,bangaren kasar Sin yana so ya yi kokari tare da bangaren kasar Zambiya don kara karfafa amincin dake tsakaninsu da kuma kara karfafa hadin guiwa dake tsakaninsu,haka kuma za a ciyar da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Zambiya gaba.
Kan dandalin hadin guiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka,Mr.Hu Jintao ya ce,dandalin hadin guiwa dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka yana ba da babbar gudumowa wajen kara karfafa shawarwarin dake tsakanin bangarorin biyu.
Mr.M Wanawasa ya sake bayyana cewa,a kullum gwamnatin kasar Zambiya tana aiwatar da manufar kasar Sin daya tak a duniya,kuma tana so ta yi kokari tare da bangaren kasar Sin don kara karfafa aminci da hadin guiwa dake tsakanin kasar Sin da kasar Zambiya.(Jamila zhou)
|