Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-14 09:06:23    
Mukaddashin shugaban kasar Zambiya ya gana da kungiyar wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin

cri
Kasar Zambiya tana dora muhimmanci ga dangantakar aminci da hadin guiwa a tsakaninta da kasar Sin, kuma tana son kara karfin irin wannan hadin guiwa a tsakanin kasashen biyu a fannin siyasa da tattalin arziki da ciniki da kuma yawon shakatawa. Malam Joackim Mwape, mukaddashin shugaban kasar Zambiya ya yi wannan kalami yayin da yake ganawa da kungiyar wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da ke karkashin jagorancin Malam Yu Zhengsheng, wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kuma sakataren kwamitin jam'iyyar a lardin Hubei na kasar a birnin Lusaka, hedkwatar kasar Zambiya a ran 13 ga wata.

A lokacin ganawar, Malam Yu Zhengsheng shi ma ya bayyana cewa, kasar Sin tana son kara yalwata dangantakar hadin kai a tsakaninta da kasar Zambiya da kuma sauran kasashe matasa don moriyar juna. Kasar Sin za ta sa kaimi ga manyan masana'antu da yawa da su zuba jari a nahiyar Afrika. (Halilu)