|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-09-07 16:58:27
|
An fara kada kuri'a a Masar don zaben shugaban kasar
cri
A yau ran 7 ga wata da safe, an fara kada kuri'a a kasar Masar don zaben shugaban kasar. Kwamitocin zabe sama da dubu 10 za su kula da kada kuri'a da kirga kuri'u a duk fadin kasar, kuma alkalai dubu 13 na kasar za su sa ido a kan zaben.
Ministan cikin gida na kasar Masar Habib Ibrahim El-Adli ya riga ya ba da umurni, inda ya nemi hukumomin tsaro na larduna daban daban na kasar da su kara karfin tsaro a dukan tashoshin tsaro da kuma kwamitocin zabe, don magance duk wani abin da zai lalata zaben.(Lubabatu Lei)
|
|
|