A ran 6 ga wata, shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya kawo karshen ziyarar abuta da ya kai wa kasar Morocco.
A ran 4 ga wata, Wu Bangguo ya isa kasar Morocco domin kawo wa kasar ziyarar aiki. A lokacin ziyararsa, Wu Bangguo ya gana da sarkin kasar da firayin ministan kasar da shugaban majalisar dattawa ta kasar da na majalisar wakilai ta kasar inda suka yi musanyar ra'ayoyinsu a kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da aikin kara yin mu'amala a tsakanin majalisun biyu da dai sauransu, kuma sun sami ra'ayi daya. An sami nasarar wannan ziyarar aiki.(Danladi)
|