Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-31 18:32:24    
Afirka ta kudu ta janye sanarwarta game da "karasa yin aikin sulhu kan hargitsin Kodivwa"

cri
A ran 31 ga wata, Ronnie Mamoepa, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Afirka ta kudu ya sanar da cewa, Afirka ta kudu ta janye sanarwar da aka bayar tun farko game da cewar "karasa yin aikin sulhu kan hargitsin Kodivwa".

A ran 30 ga wata Aziz Pahad, mataimakin ministan harkokin waje na Afirka ta kudu ya ba da sanarwar cewa, Afirka ta kudu ta riga an yi "kusan gama" aikin sulhu kan hargitsin Kodivwa, nan gaba kuma M.D.D. da kawance kasashen Afirka za su ci gaba da yin wannan aiki.

Ronnie ya ce, nufin maganar Pahad shi ne Afirka ta kudu ta kammala aikin yin sulhu na wannan mataki, ministan tsaron kasar ya yi shirin ba da rahoton aiki ga kwamitin sulhu da kawancen Afirka. Bisa ikon da M.D.D. ta danka mata ne Afirka ta kudu za ta ci gaba da yin aikin sulhu. (Umaru)