Ran 30 ga wata, majalisar dokoki ta kasar Zimbabwe ta amince da gyararren shirin tsarin mulki da gwamnatin kasar ya gabatar.
Bisa wannan gyararrren daftarin tsarin mulki, an ce, bayan da aka kwace wani fili a hukunce, to, gwamnatin kasa ne kawai zai mallaki wannan fili, Turawa masu gandun noma kuma ba su da ikon kai kara don nuna bambancin ra'ayoyinsu. Haka nan kuma gyararen daftarin nan ya gabatar da cewa, za a kafa majalisar dattijai wadda ke wakiltar moriyar sarkunan kabilu da manyan jami'ai da suka yi ritaya daga aiki da shahararrun mutane.
Malam Patrick Chinamasa, ministan shari'a na kasar Zimbabwe wanda ya gabatar da wannan gyararren daftarin tsarin mulki yana ganin cewa, daftarin nan zai kawo karshen gwagwarmar da ake yi don neman kwatar 'yancin kan Zimbabwe da yin adawa da mulkin mallaka tare da cikakkiyar nasara. (Halilu)
|