|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-08-31 08:47:06
|
Kasar Afrika ta Kudu ta bayyana cewa, an riga an kammala shawo kan rikicin Cote D'voire
cri
A ran 30 ga wannan wata, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Afrika ta Kudu Aziz Pahad ya bayyana cewa, kasar Afrika ta Kudu ta riga ta kawo karshen aikin shawo kai da ta yi kan rikicin kasar Cote D'ivore , a nan gaba, Majalisar Dinkin Duniya da kawancen kasashen Afrika za su ci gaba da ayyukan da kasar Cote D'ivore take bukata wajen gudanarwar shimfida zaman lafiya.
Mr Pahad ya yi wannan furuci ne a wannan rana lokacin da ya gana da manema labaru a birnin Pretoria, hedkwatar tattalin arziki ta kasar Afrika ta kudu. Ya shelanta cewa, a ran 31 ga wannan wata, ministan tsaron kasa na Afrika ta Kudu Mosiuoa Lekota zai gabatar da rahoton aikin shawo kai ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.(Halima)
|
|
|