A ran 29 ga wata,da kakkausar murya,gwamnatin kasar Habasha ta karyata zargin da kawancen kasashen Turai ya yi wa zaben majalisar dokokinta.
A wannan rana,a gun taron manema labaran da aka yi a birnin Abbis Ababa,babban birnin kasar Habasha,firayin ministan kasar Meles Zenawi ya bayyana cewa,zargin da kawancen kasashen Turai ya yi ba shi da tushe ko kadan,karya ce kawai.Mr.Zenawi ya ci gaba da cewa,wannan zai kawo mugun tasiri ga huldar dake tsakanin kasar Habasha da kawancen kasashen Turai.
A ran 25 ga wata,shugaban kungiyar `yan kallo kan zabe ta kawancen kasashen Turai Ana Gomes ya bayar da wani rahoto,inda ya bayyana cewa,zaben majalisar dokokin da aka yi a kasar Habasha a ran 15 ga watan Yuni na wannan shekara bai dace da ma`aunin duniya ba.(Jamila Zhou)
|