Wakilin Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 28 ga wata a birnin Luanda An Sa aya kan Wasan karate na 10 na Afrika .
A cikin gasar da aka yi , Kungiyar 'yan wasan Kasar Senegal ta ci babbar nasara . Ba kawai kasar Senegal ta zama zakaran kungiyar maza da na kungiyar mata ba har ma ta sami mindojin zinariya guda 5 na wasan mutum daya daya .
Kungiyar 'yan wasan kasar Angola ta kai matsayi na 2 na kungiyoyin maza . Congo (Brazzaville) da Kamerun sun kai matsayi na 3 tare .
Kungiyar 'yan wasan kasar Nigeria ta kai matsayi na 2 na kungiyoyin mata . Kamerun da Botswana sun kai matsayi na 3 tare . ( Ado)
|