Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-18 17:13:38    
Shugaban kasar Massar Mubaraq ya bayar da ka'idojin takarar zabi zama sabon shugaban kasa

cri
Wani labarin da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana ya bayyana cewa, a ran l7 ga watan da dare, a birnin Alkahira hedkwatar kasa, Mubaraq shugaban kasa na yanzu kuma dan takarar zama shugaban kasa na jam'iyyar al'umma da dimakuradiyyar dake kan karagar mulki ta kasar Massar ya bayar da ka'idojinsa na takarar zabe shugaban kasa.

A cikin ka'idojin takarar zabe shugaban kasa, Mr.Mubaraq ya fadi cewa, in ya ci gaba da zama shugaban kasa a karo na 5, wato cikin tsawon lokacin aikin shekaru 6 masu zuwa, s zai kara yin gyare gyare kan tsarin mulkin kasa da siyasa, Kana kuma zai kara karfin majaliar kasa wajen sa ido kan ayyukan gwamnati, Ban da haka kuma zai kara karfin sassan kula da shari'a da tsaida sabbin dokokin shari'a don yin adawa da 'yan ta'adda. A karshe dai ya yi alkawari cewa, zai yi matukar kokari don daidaita matsalar rasa aiki yi da neman bunkasuwar tattalin arziki.(Dije)