Ran 17 ga wata, a birnin Brazzaville, fadar mulkin kasar Congo Brazaville, kotun kasar ta yanke hukunci kan matsalar bacewar 'yan gudun hijira, bayan da ta kwashe makonni 3 tana bincike kan matsalar, inda aka sallami manyan hafsoshin kasar 15 wadanda a da aka zarge su da cewar suna da hannu a bacewar wasu 'yan gudun hijira.
Kotun kasar ta sallami wadannan hafsoshi ne bayan da ta ce babu isassun shaidun da ke nuna cewar suna da hannu a cikin matsalar. Amma, sabo da gwamnatin kasar ba ta aiwatar da aikin karbar 'yan gudun hijira yadda ya kamata ba, kotun kasar ta yanke hukuncin cewa, gwamnatin kasar ta biya kudin diyya na Frank na Afirka miliyan 10 ga iyalin ko wane dan gudun hijira da ya bace.(Bello)
|