
Kawancen Kasashen Afirka ya ba da wata sanarwa a birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha a ran 4 ga watan nan da dare cewa, kasashen Afirka sun ki amincewa da shirin yin kwaskwarima ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da Kawancen Kasashe 4 da kasashen Japan da India da Jamus da Brazil suka kafa ya bayar.
A gun taron musamman na karo na 4 na shugabannin kungiyar AU da aka yi a ran nan, wakilan kasashe mambobin kungiyar da yawansu ya kai kashi 90 bisa dari sun ki amicewa da shirin Kawancen Kasashe 4, suna tsayawa tsayin daka kan shirin da kungiyar AU ta tsara.?Tasallah?
|