A ran 4 ga wata,an rufe taro na biyu na duniya na kai bugu ga aikin fataucin yara dake shiyyar tsakiyar Afirka da yammacin Afirka a birnin Yaounde na kasar Cameroon.A gun taron da aka yi,an bukaci gwamnatocin kasashe daban daban na Afirka da su gama kansu don kai bugu mai karfi ga laifin fataucin yara.,ta yadda za a hana yaduwar irin wannan hali a wannan shiyya.
A gun taron da aka yi cikin kwanaki uku da suka shige,an yi tattaunawa musamman kan manufa da dabarar masu laifin fataucin yara kuma an yi nazari kan wannan don tsara matakai masu amfani don kai bugu ga irin wannan laifi a duk fadin duniya.(Jamila zhou)
|