
A ran 3 ga watan nan da sassafe an yi juyin mulkin soja a kasar Mauritania. Sojojin da suka yi juyin mulki sun riga sun mamaye fada shugaban kasa da filin jirgin sama da gidan rediyon kasa da hedkwatar 'yan sandan soja da hedkwata hafsan hafsoshi, kuma sun sarrafa Nouakchott,babban birnin kasar.
Bisa labarin da aka samu an ce, shugaban kungiyar sojojin tsaro ne ya yi juyin mulki a lokacin da shugaban kasa ya je Saudiya don halartar jana'izar shugaban kasa. (Dogonyaro)
|