Ran 2 ga wata, kungiyar EU ta bayar da wata sanarwa a birnin Bissau, fadar mulkin kasar Guinea-Bissau, inda ta yi kira ga kasar da ta gama babban zaben da take yi kamar yadda ya kamata, ta yadda za a wanzar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a kasar.
'Yan kallo na kungiyar EU suna ganin cewa, ana tafiyar da babban zaben kasar na zagaye na biyu cikin adalci, kuma an nuna hali na dimokuradiyya. Ban da wannan kuma suna fata rukunoni dabam daban na kasar za su yi kokarin neman daidaita rikicin da ke adabarsu ta hanyar doka.(Bello)
|