Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-02 09:49:15    
Salva Kiir Miyardeit ya zama mataimakin shugaba na farko na kasar Sudan

cri
A ran 1 ga wata, kungiyar neman 'yancin kan jama'ar Sudan, wato SPLM, ta zabi Salva Kiir Miyardeit a matsayin mataimakin shugaba na farko kuma shugaban gwamnatin kudu na kasar Sudan, don ya maye gurbin John Garang wanda ya mutu a hadarin jirgin sama a ran 30 ga watan jiya.

Ban da wannan, an kuma zabi Mr.Miyardeit da ya zama babban kwamandan rundunar sojojin 'yantar da jama'ar Sudan da ke karkashin jagorancin kungiyar SPLM.

A ran nan, kungiyar SPLM ta bayar da wata sanarwa, inda ta jaddada cewa, za ta ci gaba da bin yarjejeniyar shimfida zaman lafiya, kuma za ta yi kokari tare da jam'iyyar National Congress da ke karkashin jagorancin shugaba Omar al-Bashir, don tabbatar da yarjejeniyar shimfida zaman lafiya.

A ran nan kuma, babban magatakardan MDD Kofi Annan ya nuna bakin ciki sosai kan rasuwar Garang, ya kuma yi kira ga jama'ar Sudan da su ci gaba da kokarin da Mr.Garang ya yi na neman samun sulhu tsakanin kabilu da kuma shimfida zaman lafiya a Sudan. Ban da wannan, gamayyar kasashen Larabawa da kawancen kasashen Turai da dai sauran kungiyoyin duniya su ma sun nuna ta'aziyya ga rasuwar Garang a ran nan.(Lubabatu Lei)