Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-07-26 18:24:12    
Ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya gana da takwaransa na kasar Zimbabuwei

cri

A ran 26 ga wata a nan birnin Beijing, ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya gana da takwaransa na kasar Zimbabuwei Simbarashe Samuel Mumbengegwi, wanda yake raka shugaban kasar Zimbabuwei Robert Gabriel Mugabe domin yin ziyara a kasar Sin.

Li Zhaoxing ya ce, ziyarar da shugaba Mugabe yake yi a kasar Sin za ta sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar abuta da ke tsakanin kasashen biyu.

Mr Mumbengegwi ya bayyana cewa, bayan da kasar Zimbabuwei ta sami 'yancin kai, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun ba da babban taimako ga bunkasuwar kasar Zimbabuwei, jama'ar kasar ba za su manta da wannan ba. Kasar za ta dukufa wajen kara karfafa dangantakar abuta da ke tsakaninta da kasar Sin.(Danladi)