
Mun sami labari daga kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, bisa labarin da kafofin watsa labaru na Cameroon ke bayar ne a ran 24 ga wata an ce, ran 23 ga wata a Tunisia, Mr. Donald Kaberuka, sabon shugaban bankin Afrika, kuma ministan kudi da tattalin arziki na kasar Ruwanda ya bayyana cewa, a cikin wa'adin aikinsa na shekaru 5, bankin Afrika zai yi kokari kan samar da gudanarwar neman hadin kan Afrika, domin ingiza bunkasuwar tattalin arziki da kuma ci gaban zaman al'umma na babban yankin Afrika.
Mr. Kaberuka ya ce, akwai kasashe da yawa a Afrika, amma kasuwa kadan ne, tilas ne a samar da gudanarwar neman hadin kan shiyyar Afrika na gaggawa, domin kara karfin takara na Afrika a kasashen duniya.
Mr. Kaberuka ya jadadda cewa, bankin Afrika ya riga ya tsara shirye-shiryen ba da taimako ga Afrika, matsalar da ake fuskantar ita ce, yaya za a tabbatar da wadannan shirye-shirye. (Bilkisu)
|