A ran 21 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Najeriya, wato NAN ya bayar da labari cewa, gwamnatin kasar Najeriya za ta mika wa zababbiyar gwamnatin kasar Liberia tsohon shugaba Charles Taylor na kasar Liberia wanda ke neman mafakar siyasa a kasar Najeriya.
Wannan labari ya tsamo maganar da ministan harkokin waje na kasar Najeriya Mr. Oluyemi Adeniji ya yi, cewar idan zababbiyar gwamnatin kasar Liberia da za ta ci zaben da za a yi a watan Oktoba na shekarar nan ta kai Charles Taylor kara, kuma ta nemi kasar Najeriya da ta komar da Charles Taylor. Kasar Najeriya za ta komar da Charles Taylor ga gwamnatin kasar Liberia, kuma a sa'i daya, za ta sanar wa kungiyar hada kan tattalin arzikin yammacin kasashen Afirka, wato ECOWAS da Tarayyar Afirka, wato AU da wannan labari. (Sanusi Chen)
|