A ran 21 ga wata, bankin raya Afirka ya yi taron musamman a birnin Tunisiya, inda aka zabi ministan kudi da tsara shirin tattalin arziki na kasar Rwanda Dr. Donald Kaberuka sabon shugaban bankin raya Afirka. Zai maye gurbin shugaba na yanzu Mr. Omar Kabbaj, dan kasar Morocco wanda zai bar mukaminsa a watan Agusta na shekarar nan.
Yanzu, bankin raya Afirka tana da membobi 77 ciki har da membobin Afirka 53 da sauran membobi 24 da ba na Afirka ba. Ban da kasar Uganda wadda ba ta tura wakilinta zuwa taron ba, sauran membobi 76 na bankin sun aika da wakilansu zuwa taron kuma sun jefa kuri'a domin zaben sabon shugaban bankin. A cikin zaben, Dr. Kaberuka ya ci zaben da kuri'un da suka kai kashi fiye da 70 cikin kashi dari.
An haifi Dr. Kaberuka ne a arewancin kasar Rwanda a shekarar 1952. Lokacin da yake da shekaru 8 da haihuwa, shi da iyayensa sun yi gudun hijira a kasar Uganda da kasar Tanzania. Daga baya, ya sami izinin yin karatu a kasar Britaniya. A jami'ar Glasgow ta kasar Britaniya, ya sami digiri na 3 na ilmin tattalin arziki. Daga baya, ya yi aikin koyarwa da aikin yin nazari kan tattalin arziki a jami'ar Sussex da ke kudancin kasar Britaniya. Haka nan kuma, bi da bi ne ya taba yin aiki a wasu hukumomin kudi da wasu kungiyoyin kasa da kasa. A shekarar 1997, ya koma kasar Rwanda ya zama ministan kudi da tsara shirin tattalin arziki na kasar Rwanda. (Sanusi Chen)
|