A ran 21 ga wata, kungiyar kiyaye zaman lafiya ta MDD da ke kasar Kodivwa ta tabbatar da cewa, an riga an nada mataimakin wakilin MDD da ke kasar Kodivwa Alan Doss 'dan Ingila da ya zama wakilin musamman na MDD da ke kasar Liberia, domin maye gurbin tsohon wakilin wato Jacques Paul Klein, wanda ya bar aikinsa a watan Afrilu na bana.
Bisa labarin da muka samu, an ce, Mr Doss zai shugabanci kungiyar masamman ta MDD da ke kasar Liberia, kuma zai kula da harkokin 'yan gudun hijira da daidaita aikin ba da taimako da kasashen duniya suke yi wa kasar.(Danladi)
|