A ran 21 ga wata a birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan, shugaban kasar Sudan al-Bashir ya gana da sakatariyar harkokin waje na kasar Amurka Condoleezza Rice wadda ta kai wa kasar ziyarar aiki. Mr Bashir ya ce, gwamnatin kasar Sudan tana shirin yin shawarwari da dakarun Darfur da ba su ga maciji da ita domin warware matsalar Darfur cikin ruwan sanyi.
A ran nan, mataimakin shugaba na farko na kasar kuma shugaban gwamnatin kudancin kasar John Garang da ministan harkokin waje na kasar Mustafa Othman Ismail su ma sun gana da Condoleezza Rice. Malama Rice ta sanya ran alheri ga makomar dangantakar da ke tsakanin kasar Sudan da kasar Amurka.
Malama Rice ta tafi shiyyar Darfur da ke yammacin kasar Sudan inda ta zayarci barikokin 'yan gudun hijira da sojojin da kawancen kasashen Afirka ya tura a wurin domin gudanar da aikin sa ido a kan tsagaita bude wuta.(Danladi)
|