Mun sami labari daga kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, ran 19 ga wata a Libreville, shugaban majalisar wasan kwallon kafa na kasar Gabon ya bayar da sanarwar cewa, za a shirya gasar karshen cin kofin kwallon kafa na mata na Nationa Cup a kasashen Afrika na karo na 5 a birnin Libreville, babban birnin kasar Gabon a shekarar 2006.
Ya bayyana cewa, kasar Gabon za ta shirya sosai don maraba da wannan babban wasan kwallon kafa na mata a kasashen Afrika. Ya ce, a dukan kasar gabon, akwai kungiyoyin kwallon kafa na mata guda 10, amma saurin bunkasuwarsu da kuma tasirinsu ba su kai na maza ba. Shirya wanna gasa sosai a shekara mai zuwa, zai ingiza bunkasuwa da ci gaban aikin kwallon kafa na mata sosai, kuma zai sa kwallon kafa na mata ya kawo tasiri mafi girma a Afrika da dukan duniya. (Bilkisu)
|