|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2005-07-20 17:15:04
|
Kasashen Afrika suna yin amfani da fasahar jirkita kwayoyin halitta wato Jene a hankali a hankali
cri
Wakilin Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ruwaito mana labari a ran 19 ga wata cewa , Ofishin wakilan Cibiyar nazarin manufofin hatsi ta duniya dake Dakar , hedkwatar kasar Senegal ya gabatar da wani bayani , inda ya ce , wasu kasashen Afrika suna yin amfani da fasahsr jirkita kwayoyin halitta don yin bincike da gwajin wasu kayayyakin gona , ta yadda za a rage yawan magungunan kisan kwari da kara karfin kawar da fari na kayan gona da kuma kyautata Ingancin abubuwan gina jiki na mutanen Afrika .
Bayanin ya yi nuni da cewa , kasar Masar da kasar Afrika ta kudu da Kenya da Zimbabwe da sauran kasashe sun yi gwaje-gwajen fasahar jirkita kwayoyin halitta a kayayyakin gona fiye da 20 , kuma sun sami sakamako mai kyau . Shi ya sa sun zama misalin yankin Afrika a wajen yin amfani da fasahohin halitta a fannin aikin noma . (Ado)
|
|
|